Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan saka hoton masallaci a rigar mawaki

Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan saka hoton masallaci a rigar mawaki

- Biyo bayan sanya hoton masallaci a jikin rigir mawaki, shugaban masallacin ya nuna rashin jin dadinsa

- Kamfanin da ke da alhakin sanya hoton ya ba da hakuri tare da neman afuwan malaman masallacin

- Hakazalika kamfanin ya bayyana dalilin da ya sa ya sanya hoton masallacin mai duimbin tarihi

Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan sanya hoton masallaci mai dimbin tarihi a yankin Lamu na Kenya, a rigar mawakin Amurka Jay-Z, BBC Hausa ta rahoto.

Shugaban masallacin ya nuna adawarsa da rigar wanda ya ke cewa ana iya sanyata a wuraren da ake munanan ayyuka kamar mashaya.

KU KARANTA: Wani tsohon Sanatan jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya jiya Talata

Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan saka hoton masallaci a rigar mawaki
Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan saka hoton masallaci a rigar mawaki Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

"Mun karbi wasikar afuwan saboda anyi shi ne da zuciya guda," a cewar malaman masallacin.

Mai kamfanin Zeddie Loky ya ce sun sanya tambarin masallacin ne a jikin rigar domin tallata yankin Lamu.

Lamu yankin ne mai dimbin tarihi kuma masallacin da aka gina tun a karni na 19 na jan hankalin masu zuwa yawon bude ido.

An ga Jay-Z sanye da rigar da ke nuna Masallacin Riyadha na Lamu a ranar 30 ga Maris, yayin da ya fito daga wani gidan abinci a Santa Monica, California.

CNN ta ruwaito cewa, Zeddie Loky da ya zana riga T-shirt din, wanda dan kasar Kenya ne, ya sanya hotunan a shafin Instagram, lamarin da ya jawo cece-kuce.

A ranar 3 ga Afrilu, Masallacin Riyadha ya sanya rubuta zuwa Loky a shafinsa na Facebook, yana cewa kwamitin gudanarwa da masu bauta a masallacin cewa:

"sun nuna damuwa kuma a zahiri sun ji an wulakantasu" da hotunan Jay-Z sanye da T-shirt, wanda ke dauke da hoton koren hoto na masallacin, tare da kalmar "Lamu" a samansa.

KU KARANTA: Sojoji sun afkawa mafakar 'yan ta'adda, sun kashe 12 sun kwato makamai

A wani labarin, Kusan awanni 48 bayan wata Babbar Kotu a jihar Kano ta ba da umarnin hana Masarautar Kano yanka filaye a Filin Sallar Idi na 'Yar Akwa, majalisar masarautar ta ci gaba da yin hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai a farfajiyar filin ranar Asabar, shugaban kwamitin filin daga yankin, Tijjani Yahaya, ya ce sun yi mamakin cewa bayan umarnin kotu, sai kawai suka wayi gari da safe suka ga ana aikin yankan filin.

Ya bayyana cewa, ’yan sanda dauke da makamai a cikin motoci kusan biyar suna bai wa wasu mutanen da aka turo don yankan filin kariya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel