Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gini da robobin ruwa a Kaduna

Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gini da robobin ruwa a Kaduna

- Wani dan Najeriya, ya ce ya gina gida ne da robobin ruwa a matsayin wata hanya ta rage yawan shara

- Don samo robobin, dole tasa mutumin ya je wurare kamar gidajen cin abinci inda galibi ake amfani da robobi

- Ya bayyana cewa, a irin wannan gida babu bukatar AC, domin kuwa sanyi da yanayi mai kyau gareshi

Wani injiniya, Ahmed Yahaya, da ya shahara bayan yin amfani da dubban robobin ruwa wajen gina gida, ya yi karin haske game da abin da ya yi tasiri a kan shawarar da ya yanke ta fuskantar irin wannan aiki.

A hirarsa da BBC News Pidgin, mutumin ya ce ya yi amfani da robobin ruwa ne wajen tsara gidan a surar Afirka, ta yadda akwai dakuna uku da za a iya amfani da su don bukatu daban-daban.

Injiniyan ya bayyana cewa an tattara robobin da aka jefar daga wuraren zuba shara daban-daban a cikin jihar Kaduna.

KU KARANTA: Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan saka hoton masallaci a rigar mawaki

Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gina da robobin ruwa a Kaduna
Tsadar Siminti ta sa wani dan Najeriya gina da robobin ruwa a Kaduna Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa yayin tattara robobin, ba wanda ya dauke su da muhimmanci, kawai ana tambayarsu dalilin da ya sa suke ta aikin tara shara ne.

Ahmed ya bayyana cewa abin da suka sa a gaba ya jawo hankali sosai har ma mutane na son ganin yadda lamarin zai kasance.

Ya ce gina gidan yana da matukar daraja idan aka kwatanta shi da na siminti.

Da yake bayanin fa'idar gidan, ya bayyana cewa yanayin cikinsa yanayi ne mai matsakaicin sanyi.

A cewarsa, babu bukatar AC yayin rayuwa cikin irin wannan gida, ya kara da cewa gidan na adana kari kan farashin makamashi.

Ahmed ya kara da cewa ana iya yin gine-ginen zamani daban-daban da robobin ruwa bawai sai dole irin wanda ya gina ba.

Maginin ya ce irin wannan zai taimaka sosai wajen magance matsalar shara da jihar Kaduna ke fuskanta.

Kalli bidiyon inda yake bayani.

KU KARANTA: Sojoji sun afkawa mafakar 'yan ta'adda, sun kashe 12 sun kwato makamai

A wani labarin, Wasu mutane na sanya suturar suit lokacin da za su tafi ofis ko wasu lokuta na musamman, kamar biki da sauransu.

Ga wasu mutanen kuwa, - musamman 'yan sanda na sirri da sauran jami'an tsaro - suit da wando kamar inifom ne garesu, donin akan gansu dashi lokuta daban-daban.

Kamar jami'an tsaro, Zubairu Suleiman mai shekaru 24 ya yi imani da sanya suit, domin kuwa kafin ya fita aiki sai da ya tabbatar da ya shirya tsaf ya sanya kwat, wando har ma da madaurin wuya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel