'Yan sanda: Yadda muka kama Fasto mai taimakawa IPOB akai hari kan jami'an 'yan tsaro

'Yan sanda: Yadda muka kama Fasto mai taimakawa IPOB akai hari kan jami'an 'yan tsaro

- Rundunar 'yan sanda ta bayyana yadda ta kame wasu daga kungiyar IPOB da ke kashe 'yan sanda

- Rundunar ta bayyana kame wani Fasto dake baiwa 'yan kungiyar mafaka tare da filin horarwa

- Rundunar ta kame wasu mutane da bindigogi, harsashai da sauran kayayyakin aikata laifi a yankin

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani mai suna Cletus Nwachukwu Egole wanda aka fi sani da Alewa, wani fasto a cocin Holy Blessed Trinity Sabbath, da ke Orlu, a jihar Imo, dangane da harin da aka kai wa jami’an tsaro a sassan Kudu maso Gabas.

Sama da jami'an tsaro 15 aka harbe har lahira a wasu hare-hare daban-daban a cikin yankin a cikin watan Maris kadai, Daily Trust ta ruwaito.

An kona ofisoshin 'yan sanda da dama a hare-haren yayin da aka kwashe makamansu a matsayin ganima.

A wata sanarwa a ranar Lahadi, Frank Mba, ya ce an kama Egole tare da Michael Uba, wani malami na kungiyar addinin Yahudawa, da ya yi ikirarin yin aiki tare da biyu daga cikin wadanda suka shirya hare-haren.

Ya ce wadanda suka aikata wannan mummunar aikin sun yi ikirarin kasancewa mambobi ne na haramtacciyar kungiyar 'yanci ta 'yan asalin Biafra (IPOB) da kuma kungiyar tsaro ta Gabas (ESN).

KU KARANTA: Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

Yadda muka kama Fasto mai taimakawa kungiyar IPOB a hari kan jami'an 'yan sanda
Yadda muka kama Fasto mai taimakawa kungiyar IPOB a hari kan jami'an 'yan sanda Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Mba ya ce baya ga samar da asirin nasara ga kungiyar, mambobinta sun yi amfani da gidan Egole a matsayin wajen shirya munanan ayyukansu sannan kuma ya ba da gonar dan uwansa da ya mutu don amfani da ita a matsayin maboya da sansanin horarwa ta kungiyar.

Ya bayyana sunayen mutane biyun da ake zargi da suna Ugochukwu Samuel da aka fi sani da Biggy, dan shekara 28 kuma dan asalin karamar hukumar Arochukwu ta jihar Abia da kuma Raphael Idang dan shekara 31, daga karamar hukumar Odukpani ta jihar Kuros Riba.

“Sauran mutane goma sha biyu, yayin gudanar da bincike, an gano suna da hannu a cikin manyan laifuka da aka aikata a fadin jihohi da yawa a yankin Kudu maso Gabashin kasar.

“An kama wadanda ake zargin a yankuna daban-daban na kasar bayan ci gaba, da kuma gudanar da ayyukan sirri na jami'ai.

“Binciken 'yan sanda ya bayyana karara kuma ya alakanta wadanda ake zargin da yawaitar hare-hare da kisan jami’an tsaro tare da sata, mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, konawa da kuma mummunar barna ga kadarorin aiki na sojoji da jami’an tsaro.

“Bincike ya nuna cewa Ugochukwu Samuel, wanda aka fi sani da Biggy, da kuma Raphael Idang suna daga cikin masu laifin da suka afkawa 'yan sanda da ke bakin aiki a wani shingen bincike a ranar 24 ga Disamba, 2020 a kan titin Orlu-Ihiala a Jihar Imo.

“Bugu da kari, dukkansu suna daga cikin wata babbar kungiya da ta kaiwa tawagar 'yan sandan leken asiri hari a ranar 13 ga Janairu, 2021 inda suka kashe wani dan sanda guda.

"Ugochukwu Samuel da aka fi sani da Biggy, wanda ya samu raunin harsashi a yayin wani hari da kungiyarsa ta kai wa ayarin sojoji inda aka kashe wasu sojoji tare da kwashe makamai, daga baya aka kame yayin da yake karbar kulawa a asibiti.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano

"Dukkanin wadanda ake zargin sun furta cewa su mambobin IPOB da ESN ne,” in ji Mba a cikin sanarwar.

Ya kara da cewa an kwato bindigogin AK47 guda tara, wasu manyan bindigogi guda biyar, Mujallun AK47 guda 17, harsasai 549 na AK47, kayan hada abubuwa masu fashewa guda 10 (IEDs), rigunan kariya na harsashi, kayayyaki da sauran abubuwan aikata laifi.

Membobin ESN sun yi bata kashi da jami'an tsaro a rikicin da ya kai ga kashe mutane da yawa, ciki har da fararen hula da jami'an tsaro, a yankin Orlu na jihar Imo.

A wani labarin, Akalla mambobin Cocin Redeemed Christian Church of God takwas yan bindiga suka sace a Kaduna, a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa wadanda lamarin ya rutsa da su suna cikin motar cocin ne suna tafiya domin halartan wani taro lokacin da aka kai musu harin.

Legit.ng ta tattaro cewa wani mai amfani da Facebook, Eje Kenny Faraday, ya sanar da labarin a shafinsa tare da hoton farar motar a yammacin ranar Juma'a, 26 ga Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.