Har Yanzu jam'iyyar APC ba ta shiga Next Level ba, Inji Gwamna Ganduje
- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce har yanzun jam'iyyarsu ta APC ba ta shiga mataki na gaba ba wato Next Level
- Gwamnan ya misalta jam'iyyar da karatun Chemistry inda ya ce har yau jam'iyyar na nan a cuɗe bata zama cikakkiyar guda ɗaya ba.
- Ganduje ya yi wannan furuci ne a wani taro da kwamitin duba da gyaran kundin tsarin jam'iyyar na Arewa maso yamma ya shirya a jihar Kano
Gwmnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce shekaru bakwai kenan da kafa jam'iyyar APC amma har yanzin ba ta zama haɗaɗɗiyar jam'iyya ba.
Gwamnan ya bayyana jam'iyyar da cuɗuwar jam'iyyun siyasa da suke faman ganin sun zama jam'iyya ɗaya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: An bankado badakalar kadarorin wasu tsoffin gwamnoni da sanatatoci a Dubai
Ganduje ya yi wannan jawabi ne a wani taro da kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin APC na yankin arewa maso yamma ya shirya a jihar Kano.
An ƙirƙiri jam'iyyar APC ne a shekarar 2013 bayan haɗin guiwar jam'iyyu kamar; CPC, ANPP, nPDP, APGA da kuma ACN, waɗanda suka haɗu wuri ɗaya don ganin sun ƙwace mulki.
A zaɓen shekarar 2015, jam'iyyar ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da kuma na mafi yawancin jihohin ƙasar nan da yan majalisu.
Hakanan jam'iyyar ta APC ta sake kai banten ta a zaɓen 2019, sai dai daga baya rikice-rikice sun addabi jam'iyyar, wanda hakan yakai ga rushe shugabancin Adams Oshiomhole.
Gwamnan Kano, Ganduje ya ce:
"APC jam'iyya ce da ta fara da cuɗanyar jam'iyyu kamar; CPC, ANPP, ACN, nPDP da AFGA. Wannan cuɗanyar abubuwa ne da dama da suke ƙoƙarin samar da wani abu."
"Abin takaicin shine har yanzun APC a cuɗe take, bata shiga mataki na gaba ba (Next Level) wato ta zama abu ɗaya."
Gwamnan ya ce Idan kai ɗalibin Chemistry ne to kasan banbanci tsakanin cuɗaɗɗen abu (mixture) da kuma Compoud.
KARANTA ANAN: 'Yan bindiga na kai hari Kaduna ne saboda mun ki basu kudi, gwamna El-Rufai
Ya ƙara da cewa Mixture wani abu ne da zaka iya rarraba shi cikin sauƙi amma compoud duk wani sashi daka cire to bazai canza ba, yana nan yadda ya ke.
Daga ƙarshe gwamnan ya ce yana fatan gyaran kundin tsarin jam'iyyar ya fi karkata akan waɗannan matsalolin don a sami tsayayyar APC.
Anasa jawabin shugaban kwamitin duba kundin tsarin jam'iyyar na yankin arewa maso yamma, Dr Tahir Mamman, ya ce duk wani tsari da ya ɗauki tsawon shekaru 7 zuwa 8, to akwai yuwuwar a sami wasu matsaloli a cikinsa.
Ya kuma ƙara da bayyana cewa wannan taron yazo a lokacin da ya dace.
A wani labarin kuma Yan Sanda sun cafke wani da ake zargin ɗan garkuwa ne da AK-47 a jihar Kano
Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama wani mutumi da ake zarginsa da aikata laifin garkuwa da mutane
Yan sandan sun sami bindigu har guda biyu AK-47 a wurin wanda suka kama ɗin, amma ya ce ba nashi bane a hannun wasu yan Zamfara ya same su.
Asali: Legit.ng