Yan Sanda sun cafke wani da ake zargin ɗan garkuwa ne da AK-47 a jihar Kano

Yan Sanda sun cafke wani da ake zargin ɗan garkuwa ne da AK-47 a jihar Kano

- Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama wani mutumi da ake zarginsa da aikata laifin garkuwa da mutane

- Yan sandan sun sami bindigu har guda biyu AK-47 a wurin wanda suka kama ɗin, amma ya ce ba nashi bane a hannun wasu yan Zamfara ya same su

- Mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar Kano ya tabbatar da kama wanda ake zargin amma ya ce zasu gurfanar dashi a kotu zarar sun gama bincike

Hukumar yan sanda a jihar Kano ta kama wani da ake zargin ɗan garkuwa da mutane ne, Abubakar Burumburum ɗan kimanin shekara 27.

KARANTA ANAN: Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle na shirin komawa APC gabannin zaben 2023

Jami'an yan sanda na 'Operation Puff Adder' sun kama mutumin da bindigu guda biyu ƙirar AK-47, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ga manema labarai ran Lahadi.

Haruna ya ce mutumin da aka kama, wanda aka fi sani da suna Likita a yankin Birnin Gwari, yana gudanar da aikinsa a jihohin Kano, Kaduna da sauran sassan arewa maso yamma.

Yan Sanda sun cafke wani da ake zargin ɗan garkuwa ne da AK-47 a jihar Kano
Yan Sanda sun cafke wani da ake zargin ɗan garkuwa ne da AK-47 a jihar Kano Hoto: @PoliceNG_CRU
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga- zangar tsirara a fadin kudu maso gabas

A lokacin da yake amsa tambayoyi, Burumburum, wanda uba ne mai 'ya'ya shida a karamar hukumar Tudun Wada, jihar Kano, ya amsa laifinshi da cewa yana satar shanu amma ya taɓa yin garkuwa da mutane sau biyu kacal.

Burumburum ya ce, bindigun da aka samu a hannunshi guda biyu kirar AK-47 ya same su ne a wajen 'ya'yan wani mutumi da ya rasu, Muhammadu Bakanoma, a jihar Zamfara.

Sai dai mai magana da yawun yan sanda ya ce bada jimawa ba zasu gurfanar da Burumburum a gaban ƙuliya da zarar sun gama gudanar da bincike.

A wani labarin kuma Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun Kashe 'yan kasuwa 7 Yan Arewa a jihar Imo

An shiga cikin yanayin tashin hankali a jihar Imo bayan kisan wasu yan kasuwa 7 yan Arewa da aka yi a cikin kwana biyu.

Shaidun gani da ido sun tabbatar a aukuwar lamarin, kuma sun ce mutanen da aka kashe sun daɗe suna rayuwa a yankin ba tare da wata matsala ba.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel