'Yan bindiga na kai hari Kaduna ne saboda mun ki basu kudi, gwamna El-Rufai

'Yan bindiga na kai hari Kaduna ne saboda mun ki basu kudi, gwamna El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana dalilan da yasa 'yan bindiga ke kai hari jihar ta Kaduna

- Ya ce, hare-haren 'yan bindigan na da nasaba da kin tattaunawa da gwamnatin jihar ta kudurta

- Ya kuma ce, dolene a shafe dukkan masu aikata laifi ba wai a zauna zaman tattaunawa dasu ba

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ‘yan bindiga da masu satar mutane suna kai hari jihar ne saboda matsayin gwamnati na kin tattaunawa da masu aikata laifi.

El-Rufai, wanda ya yi magana ta manhajar Zoom a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels a daren jiya, ya ce gwamnatin jihar ba za ta sauya matsayinta a kan batun ba, yana mai cewa ba wayewa ba ce ta tattaunawa da masu laifi.

Ya bayyana wadanda ke daukar zabin tattaunawa da 'yan bindigan a matsayin marasa hankali da kuma son tayar da hankali.

KU KARANTA: Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka kubutar da fursunoni sama da 2,000 daga magarkama

'Yan bindiga na kai hari Kaduna ne saboda mun ki basu kudi, gwamna El-Rufai
'Yan bindiga na kai hari Kaduna ne saboda mun ki basu kudi, gwamna El-Rufai Hoto: icirnigeria.org
Asali: UGC

Ya ce: "Ina tsammanin 'yan bindiga da shugabanninsu sun yanke shawarar hada baki su nufi jihar Kaduna ne saboda matsayin da muke kai na ba za mu tattauna da su ba, cewa ba za mu ba su ko da kwabo na kudin masu biyan haraji ba.

“Kuma duk wanda ya zo Kaduna da nufin sata ko satar mutane to tabbas zai mutu.

“Mun yi imanin cewa mafita ga wannan matsalar ita ce ta kara kaimi ga ayyukan soji daga sama ko kasa tare da shafe su baki daya. Ba ma tsammanin wani dan bindiga ya cancanci rayuwa.”

Gwamnan ya ce, hanya daya tilo a don magance masu aikata laifuka ita ce a yi amfani da cikakken nauyin doka.

“Babu wata al’umma mai wayewa da za ta zauna bayan an kalubalanci ikon mulkinta, lokacin da aka kalubalanci ikon mallakarta na tilastawa.

"Abu na farko da za'ayi shine a shafe wadannan 'yan bindigan. Wannan yaki ne, dole ne mu yake su mu ga karshensu. Dole ne mu shafe su. Wannan shi ne tsari na farko na halin da ake ciki.

“Lokacin da kuka shafe 95% daga cikinsu, idan 5% a shirye suke su tuba su koma rayuwar farar hula ta yau da kullun, to za mu iya tattaunawa amma ba a magana da masu laifi a lokacin da suka fara.

"Babu wani zabi. Babu wata al'umma da ke zaune tare da tattaunawa da masu aikata laifi, babu a ko'ina cikin duniya. Kuna basu karfin gwiwa ne, kuna karfafa masu gwiwa ne,” in ji El-Rufai.

Dangane da sace dalibai 39 daga Kwalejin Koyon Ilimin Noma da Gandun Daji ta Tarayya, Afaka da ke Kaduna a ranar 11 ga Maris 2021, El-Rufai ya ce gwamnatin jihar tana amfani da kayan fasaha wajen gano daliban da aka sace tare da bin ‘yan bidnigan.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun fasa gidan yari da hedkwatar 'yan sanda, fursunoni sun tsere

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wani fitaccen malamin addini a Arewa, Sheikh Ahmad Gumi, sun ba da shawarar kafa kotuna na musamman da za su yi shari’ar ’yan bindiga, masu satar mutane da masu safarar muggan makamai a Najeriya.

Obasanjo da Gumi sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka sanya hannu bayan sun yi wata ganawar sirri a dakin karatun Obasanjo dake Abeokuta a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

A wani bagnaren sanarwar, ance; “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki batun da muhimmanci a tsakanin ECOWAS don yin aiki a magance matsalar yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel