Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka kubutar da fursunoni sama da 2,000 daga magarkama

Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka kubutar da fursunoni sama da 2,000 daga magarkama

- 'Ya bindiga sun far wa gidan yari a jihar Imo inda suka kubutar da fursunoni sama da 2,000

- Sun kuma afkawa hedkwatar rundunar 'yan sanda na jihar, inda suka barnata motoci da dama

- Ana zargin 'yan kungiyar ESN na Biafra ne suka kai harin, sai dai har yanzu ba a tabbatar ba

Wasu ‘yan bindiga sun saki akalla fursunoni 2,000 a hedikwatar Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya (NCS) dake Owerri a Jihar Imo.

'Yan bindigan sun kuma kai hari ofishin da ke kusa da sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) na rundunar 'yan sandan jihar, tare da sakin wadanda ake zargi a wurin.

Maharan sun kona kusan dukkan motocin da ke ajiye a hedikwatar sannan kuma suka kubutar da dukkan wadanda ake zargi a kusan dukkanin sassan da ke SCID din.

SaharaReporters ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi barnar ne a cikin motoci fiye da 10, sannan kuma sun kai hari kan sojoji da ke Umuorji a kan babbar hanyar Owerri zuwa Onitsha.

KU KARANTA: Obasanjo ya bi sahun Gumi, ya roki gwamnatin Buhari ta yafewa tubabbun 'yan bindiga

Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka kubutar da fursunoni sama da 2,000 a jihar Imo
Hoto: bbc.com
Karin bayani: Yadda 'yan bindiga suka kubutar da fursunoni sama da 2,000 a jihar Imo
Asali: UGC

An ce maharan sun dauki kimanin awanni biyu suna barnar kuma sun fara ne tsakanin karfe 1 na safe zuwa 2 na safiyar Litinin.

An samu labarin cewa ‘yan bindigar sun haifar da fargaba a garin yayin da aka ji karar fashewar abubuwa a kusa da hedikwatar rundunar 'yan sanda ta jihar da kuma cibiyar NCC da ke Owerri.

“An samu fashin magarkama a gidan yari na Owerri da misalin karfe 4 na asuba bayan da ‘yan bindigan suka kai hari. An kira sojoji don su tsare wurin amma fursunoni da yawa sun gudu,” in ji wata majiya.

An yi zargin cewa maharan jami'ai ne na kungiyar tsaro ta Gabas da kungiyar tsagerun yankin Biafra ta kafa amma har yanzu ba a tabbatar da hakan ba.

A wani faifan bidiyo da SaharaReporters ta samu, ‘yan bindigar sun cinna wa ofishin 'yan sanda wuta yayin da suke ci gaba da harbe-harbe.

Wata majiya ta ce, “Wannan shi ne abin da ya biyo bayan barna na 'yan bindigan da ake zargin 'yan ESN ne a hedikwatar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar Imo lokacin da 'yan bindigan suka far wa hedikwatar ‘yan sanda.

"Sun kuma je magarkamar tarrayar Najeriya tare da 'yanta fursunoni; duk wadannan sun faru ne a daren jiya.”

Wannan shi ne hari na biyar da aka kaiwa hedkwatar ‘yan sanda a fadin jihar.

KU KARANTA: Yadda 'yan Biafra masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga a safiyar ranar Litinin sun kai hari a gidan yari na Owerri da ke cikin babban birnin jihar Imo tare da kubutar da fursunoni sama da 1500.

Maharan sun kuma kone hedikwatar rundunar 'yan sanda ta jihar Imo da ke Owerri tare da kona kusan dukkanin motocin da ke ajiye a helkwatar rundunar.

'Yan bindigar sun ci gaba da sakin wadanda ake zargin a kusan dukkanin magarkamu a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel