Sheikh Gumi da Obasanjo sun shawarci gwamnati da ta kirkiri kotun 'yan bindiga

Sheikh Gumi da Obasanjo sun shawarci gwamnati da ta kirkiri kotun 'yan bindiga

- Tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo ya gana da Sheikh Gumi kan batun matsalar tsaro

- Fitattun biyu sun shawarci gwamnatin tarayya da ta kirkiri wasu kotuna don hukunta 'yan bindiga

- Sun kuma jaddada goyon bayansu ga tallafawa kasar a yaki da take da matsalar rashin tsaro

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wani fitaccen malamin addini a Arewa, Sheikh Ahmad Gumi, sun ba da shawarar kafa kotuna na musamman da za su yi shari’ar ’yan bindiga, masu satar mutane da masu safarar muggan makamai a Najeriya.

Obasanjo da Gumi sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka sanya hannu bayan sun yi wata ganawar sirri a dakin karatun Obasanjo dake Abeokuta a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

A wani bagnaren sanarwar, ance; “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki batun da muhimmanci a tsakanin ECOWAS don yin aiki a magance matsalar yankin.

KU KARANTA: Yanzun-yanzu: Kasar Indiya ta ba Najeriya gudunmawar rigakafin Korona 100,000

Sheikh Gumi da Obasanjo sun shawarci gwamnati da ta kirkiri kotun 'yan bindiga
Sheikh Gumi da Obasanjo sun shawarci gwamnati da ta kirkiri kotun 'yan bindiga Hoto: shgl.tv
Asali: UGC

“Kowace al’umma dole ne a karfafa ta kuma a ba ta karfin gwiwa don tsayawa tsayin daka da karfi kan masu laifi.

“Ya kamata a samu kariya da tukuici a boye ga masu tsegunta masu laifi da ke rayuwa a cikin alumma.

“Ya kamata a kirkiro kotuna na musamman don tunkarar shari’ar 'yan bindiga, satar mutane, neman kudin fansa da kuma daukar makamai ba bisa ka’ida ba.

“Ya kamata taken ya zama: Tsaro nauyi ne da ke wuyan dukkan 'yan Najeriya.

"Mun yarda da ci gaba da yin aiki tare don samar da mafita ga tsaron Najeriya da kuma neman wasu su kasance tare da mu kamar yadda muke yada bayanan hadin gwiwarmu a fili”

KU KARANTA: Duk da umarnin hani daga kotu, masaurautar Kano ta fara yanka filin Idin 'Yar Akwa

A wani labarin, Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya kai ziyara ga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, Jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa shahararren malamin na can a yanzu haka sun gudanar da taro da Obasanjo.

An ruwaito cewa malamin ya isa gidan tsohon shugaban ƙasar dake garin Abeokuta da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.