Yan bindiga sun kashe akalla mutum 2600, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle

Yan bindiga sun kashe akalla mutum 2600, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle

- Matsalar tsaro ta zama babban kalubale ga shugabannin Najeriya

- Bayan rikicin Boko Haram a Arewa maso gabas, rikicin tsagerun yan bindiga ya galabi jama'a

- An yi rashin dubunnan rayuka da har yanzu ba'a takamammen adadinsu ba

Gwamnan Bello Matawalle na jihar Zamfara bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta ke sulhu da yan bindiga, inda yace sulhu kadai ne mafita daga matsalar tsaron jihar.

Gwamnan ya yi bayanin cewa tsakanin 2011 da 2019, yan bindiga sun hallaka mutum 2,619, sun yi garkuwa da 1,190 kuma sun karbi akalla N970 million matsayin kudin fansa daga wajen iyalan wadanda suka sace.

Matawalle ya bayyana hakan ne ta bakin kwamishanan labaran, Ibrahim Dosara, a Kaduna ranar Juma'a, rahoton Punch.

A cewar Dosara, Matawalle ya zabi sulhu da tsagerun yan bindigan shine don kare rayukan al'ummarsa da dukiyoyinsu.

Yace: "Gabanin hawa mulkin Bello Mohammed Matawallen Maradun a ranar 29 ga Mayu 2019, mutan Zamfara na cikin halin ha'ula'i sakamakon hare-haren yan bindiga."

"Kashe-kashe, sace-sace, da fyade sun zama ruwan dare."

KU KARANTA: Da duminsa: Dan majalisar wakilai ya mutu a hadarin mota

Yan bindiga sun kashe akalla mutum 2600, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle
Yan bindiga sun kashe akalla mutum 2600, sun karbi kudin fansan kimanin N1bn: Matawalle Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan

A bangare guda, Gwamnan Matawalle, ya bayyana cewa akwai kimanin yan bindiga 30,000 a jiharsa da kuma wasu jihohin Arewacin Najeriya biyar.

A cewar gwamnan, akwai akalla sansanonin tsagerun yan bindiga 100 kuma kowace sansani na da akalla yan bindiga 300.

Asali: Legit.ng

Online view pixel