Abin Da Yasa Na Fi son Auren 'Yan Mata, Attajirin Mai Kudi, Ned Nwoko

Abin Da Yasa Na Fi son Auren 'Yan Mata, Attajirin Mai Kudi, Ned Nwoko

- Attajirin dan Nigeria, Cif Ned Nwoko ya ce ya gwammace ya auri mata fiye da daya ne saboda saukin kashe kudi

- Tsohon dan majalisar tarayyar ya ce duk da mata daya yan kudu ke aura, zaka tarar suna da yan mata a waje kimanin 10

- Jigon na jam'iyyar PDP ya kuma ce auren mata fiye da daya yana taimakawa al'umma rage mata masu yawon bin maza

- Nwoko ya yi korafi kan yadda wasu yan kudu suka yi watsi da al'adarsu ta asali da ta bada damar auren mata fiye da daya

Biloniyan Nigeria kuma tsohon dan majalisar taraya, Cif Ned Nwoko, ya yi bayanin abin da yasa ya ke da matan aure fiye da daya kuma ya fi son auren 'yan mata.

A hirar da BBC Igbo ta yi da shi a ranar Laraba, jigon na PDP ya ce batun tattalin arziki ne yasa ya ke auren mata fiye da daya, Vanguard ta ruwaito.

Abin da yasa na fi son auren 'yan mata, Attajirin mai kudi, Ned Nwoko
Abin da yasa na fi son auren 'yan mata, Attajirin mai kudi, Ned Nwoko. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi

Nwoko, mijin jaruman Nollywood Regina Daniels ya ce galibin dan arewa yana da mata a kalla guda biyu wanda ya ce hakan na hana mata yawon bin maza barkatai.

"Amma duk da cewa addinin kirista ba amince namiji ya auri mata fiye da daya ba, za ka ga namiji daya a kudu yana da yan mata 10."

Dan siyasan ya ce auren mata fiye da daya da yan arewa ke yi ya taimaka musu wurin hayayyafa hakan yasa su ke da rinjaye a kasar.

Nwoko ya koka kan yadda wayewa na zamani ke saka maza na auren mata daya duk da cewa ba al'adar mu bane.

KU KARANTA: Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su

Ya ce: "Ina son al'adun mu kamar yadda na san shi, ba kamar yadda suke son sauya abin ba. Al'addar Ibo mai kyau ne sosai kuma ya kamata a habbaka shi a yadda ya ke.

"Amma idan ka kalli yawan mutanen Nigeria da abinda na ke kira tattalin arzikin aure, a matsayin dan ibo mai mata daya da yara hudu, dan arewa mai mata hudu, kowannensu na da yara biyar, a shekaru 10 nan gaba, ko 20, ya kake tunanin yawan yan arewa zai kasance."

Asali: Legit.ng

Online view pixel