Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun afkawa gidan tsohon ministan wasanni a Filato

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun afkawa gidan tsohon ministan wasanni a Filato

- Rahoto ya shaida cewa, a daren ranar Laraba 'yan bindiga sun kai hari gidan Damishi Sango

- Sango ya kasance tsohon ministan wasanni dan asalin jihar Filato a arewacin Najeriya

- A yayin harin an harbe jami'an tsaro biyu da wani yaro, an kuma gudu da bindigigon jami'an

'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon Ministan Wasanni, Damishi Sango, da ke jihar Filato.

Jaridar The Nation ta samu labarin sun kai hari gidan nasa da ke Danwal, Ganawuri bayan Vom, a karamar hukumar Riyom da misalin karfe 9:00 na daren Laraba.

A cewar rahotanni, an harbe wasu jami'an tsaro biyu da wani yaro yayin harin.

An kuma fahimci cewa 'yan bindigar sun tafi da bindigogin jami'an.

KU KARANTA: Jami'an kwana-kwana uku da wasu sun jikkata a wata gobara a Kaduna

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun afkawa gidan tsohon ministan wasanni a jihar Filato
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun afkawa gidan tsohon ministan wasanni a jihar Filato Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sanda ta Filato, ASP. Gabriel Ubah, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce: “Rundunar 'yan sanda na sane da faruwar lamarin a Riyom kuma an garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibiti inda suke karbar magani.

“Ban sani ba tukuna ko an kwace bindigoginsu.

"Tawagar masu bincike da jami'an leken asiri tuni suka fara bincike tare da farautar masu laifin."

Ya ba da tabbacin cewa tsohon Ministan da danginsa suna cikin koshin lafiya kuma ba a samu rauni ba.

KU KARANTA: APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba

A wani labarin, Akalla mutane takwas ne suka mutu, wasu hudu kuma suka ji rauni sakamakon wasu ‘yan bindiga da suka kai hare-hare daban-daban a kan kananan hukumomin Chikun, Giwa da Kajuru na jihar Kaduna, Daily Nagerian ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, ya bayyana abubuwan da suka faru a rahotannin da hukumomin tsaro suka gabatarwa gwamnati.

"A Kan Hawa Zankoro, kusa da Unguwan Yako a karamar hukumar Chikun, wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun harbi wata mota, daga nan kuma sai ta tarwatse, ta kai ga mutuwar mutane shida, sannan wasu hudu suka ji rauni," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel