Jami'an kwana-kwana uku da wasu sun jikkata a wata gobara a Kaduna

Jami'an kwana-kwana uku da wasu sun jikkata a wata gobara a Kaduna

- Wata gobara da ta tashi a jihar Kaduna ta yi sanadiyyar raunata jami'an kwana-kwana uku

- An ruwaito cewa, wasu mutane dake kokarin kare dukiyoyinsu su ma sun jikkata a wurin

- Tuni hukumar kashe gobara ta kashe wutar ta kuma dauki jami'anta uku zuwa asibiti

An samu firgici lokacin da 'yan kwana-kwana uku da wasu mazauna gari suka samu raunuka sakamakon wata gobara da ta tashi a jihar Kaduna.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a yankin Bushara da ke kan babbar hanyar Nnamdi Azikwe ranar Talata a wani garejin tanka da ke kusa.

An samu labarin cewa wutar ta dauki tsawon awanni uku kafin daga karshe jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka kashe ta.

KU KARANTA: Najeriya da Dubai sun bankado masu turowa 'yan Boko Haram kudade daga waje

Jami'an kwana-kwana uku da wasu sun jikkata a wata gobara a Kaduna
Jami'an kwana-kwana uku da wasu sun jikkata a wata gobara a Kaduna Hoto: dailytimes.ng
Asali: UGC

Cikakkun bayanai game da tashin gobarar na ci gaba da zama a harde saboda tankunan da ke kone kurmus ciki har da wasu kalilan din shagunan kusa da garejin.

Wakilin Daily Trust da ya ziyarci wurin a ranar Laraba ya ruwaito cewa an ga mutane a gungu-gungu suna tattauna faruwar bala'in.

Wani ma'aikacin kabu-kabu da bai ambaci sunansa ba ya shaida cewa mutane da yawa sun samu raunuka yayin da suke kokarin cire motocinsu daga garejin.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar, Nathaniel Gaya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce uku daga cikin mutanensu na daga cikin wadanda suka jikkata.

A cewarsa, an garzaya da jami’an uku zuwa asibiti.

Ya ce har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba amma ya bayyana cewa ma'aikatan da suka jikkata na kwance a asibiti.

KU KARANTA: Babu wanda ya dauki Buhari da muhimmanci, hatta shugabannin hafsun soji, wani sanata

A wani labarin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce kawo yanzu an tara zunzurutun kudi har Naira miliyan 170 daga masu hannu da shuni da sauran ‘yan Najeriya mutanen kirki, a matsayin gudummawa ga wadanda iftila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina.

Masari ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar dattawan Katsina karkashin jagorancin shugabanta, Ahmad Muhammad-Daku a gidan gwamnatin Katsina, ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Kodayake har yanzu ba mu bude kofofin don ba da gudummawa ga wadanda bala'in gobarar ya shafa ba, mun kaddamar da kwamiti don gano musabbabin tashin gobarar", in ji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.