Mutum 8 sun mutu, 4 sun ji rauni a harin 'yan bindiga a jihar Kaduna

Mutum 8 sun mutu, 4 sun ji rauni a harin 'yan bindiga a jihar Kaduna

- Hukumar tsaro a jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar wasu mutane 8 a yankunan jihar

- An bayyana cewa, 'yan bindiga sun hari wasu yankunan jihar suka kuma kashe mutane da dama

- A yanzu haka akwai wadanda suka ji rauni a hare-haren da ke karbar kulawar asibiti a cikin jihar

Akalla mutane takwas ne suka mutu, wasu hudu kuma suka ji rauni sakamakon wasu ‘yan bindiga da suka kai hare-hare daban-daban a kan kananan hukumomin Chikun, Giwa da Kajuru na jihar Kaduna, Daily Nagerian ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, ya bayyana abubuwan da suka faru a rahotannin da hukumomin tsaro suka gabatarwa gwamnati.

"A Kan Hawa Zankoro, kusa da Unguwan Yako a karamar hukumar Chikun, wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun harbi wata mota, daga nan kuma sai ta tarwatse, ta kai ga mutuwar mutane shida, sannan wasu hudu suka ji rauni," in ji shi.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirya kashe N396bn kan rigakafin Korona, Ministar Kudi

Mutum 8 sun mutu, 4 sun ji rauni a harin 'yan bindiga a jihar Kaduna
Mutum 8 sun mutu, 4 sun ji rauni a harin 'yan bindiga a jihar Kaduna Hoto: flavision.com
Asali: UGC

Wadanda suka rasa rayukansu a harin sun hada da Aisha Bello, Uwaliya Alhaji Shehu, Ramatu Sani, Muhammad Shehu, Aminu Ibrahim da kuma Ibrahim Abdu.

A cewar Mista Aruwan, wadanda suka samu raunuka sun hada da Zainab Alhaji Usman, Surayya Bello, Khalifa Sani da Ushe Sani.

A wani labarin kuma, 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun far wa mazauna yankin Iburu a karamar hukumar Kajuru, suka kashe wani mai suna Amos Yari.

Bugu da kari, 'yan bindiga sun mamaye kauyen Hayin Kanwa, gundumar Fatika, karamar hukumar Giwa, suka harbe wani Alhaji Sule; dan kasuwa a yankin, bayan da ya bijirewa yunkurinsu na sace shi.

Gwamna Nasiru El-Rufai ya karbi rahotannin da bakin ciki, sannan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda aka kashe, tare da aika sakon ta’aziyya ga danginsu. Ya kuma yiwa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

KU KARANTA: Gobarar kasuwar Katsina: An tara gudunmawar N170m zuwa yanzu, in ji gwamna Masari

A wani labarin, Wasu mahara dauke da bindiga sun kaddamar da wani hari a tsakar dare a garin Kojoli da ke karamar hukumar Jada a jihar Adamawa inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin biyu, jaridar Punch ta ruwaito.

Wani dan asalin garin, Dokta Umar Ardo, ya ce ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin karfe 1 na safiyar Lahadi kuma suka yi awon gaba da wasu fitattun mutane biyu bayan sun fatattaki 'yan banga da ke yankin.

“A karo na sama da goma, 'yan bindiga a safiyar yau sun mamaye mahaifata, Kojoli. Sun afkawa Banja, wani yankin da galibi fulani suke zaune, cikin adadi mai yawa dauke da manyan bindigogi, cikin sauki suka fi karfin 'yan banga na yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.