'Yan Najeriya sun yi wa Buhari zanga zanga a hanyar shiga gidansa na Landan

'Yan Najeriya sun yi wa Buhari zanga zanga a hanyar shiga gidansa na Landan

- Yan Najerya mazauna kasar Birtaniya sun gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin Najeriya

- Sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya koma kasarsa yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da ke birnin Landan

- Hakan na daga cikin adawa da suke yi da tafiyar Buhari Birtaniya domin a duba lafiyarsa yayinda kasar ke cikin wani yanayi

A ranar Laraba, 31 ga watan Maris ne wasu ’yan asalin Najeriya mazauna kasar Birtaniya, suka gudanar da zanga-zanga a kan Shugaba Muhammadu Buhari, inda suka nemi ya koma gida.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa wasu ’yan Najeriya a Birtaniya sun taru a kofar gidan Gwamnati Najeriya da ke birnin Landan sannan kuma suka tare hanyar shiga ciki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An damke sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Nijar

'Yan Najeriya sun yi wa Buhari zanga zanga a hanyar shiga gidansa na Landan
'Yan Najeriya sun yi wa Buhari zanga zanga a hanyar shiga gidansa na Landan Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Masu zanga-zangar sun kasance dauke da kwalaye inda suka rika kira ga Shugaban kasar na Najeriya da ya koma kasarsa yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da ke birnin Landan.

Sun kirkiro maudu'i a shafin Tuwita mai taken #BuhariMustGo, wato dole Buhari ya sauka daga mulki, domin nuna bacin ransu kan abin da suka kira rashin iya gudanar da mulkinsa.

Da dama daga cikin al’ummar Najeriya sun bayyana bacin ransu kan tafiiyar Buhari kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa.

Wasu sun kira hakan a matsayin barnatar da kudin talakawan kasar masu biyan haraji yayin da wasu kuma ke sukar gazawar gwamnatin na inganta harkokin kiwon lafiyar da suka tabarbare, jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Barayi sun afka gidan jarumin Kannywood, sun yi awon gaba da sabuwar motarsa da wasu muhimman kayayyaki

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a jamhuriyyar Nijar.

Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana alhinin shugaban a jawabin da ya saki da yammacin Laraba.

Buhari yace "ba zai yiwu wasu su yi kokarin tunbuke gwamnatin da jama'a suka zaba ba a dukkan kasashen duniya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng