Najeriya da Dubai sun bankado masu turowa 'yan Boko Haram kudade daga waje
- Gwamnatin Najeriya ta hada kai da UAE don tabbatar da bankado masu daukar nauyin ta'addanci
- Kasashen biyu suna kan bincike don bankado wadanda ke tura kudade ga 'yan Boko Haram
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, shaidu sun tabbata kuma har an kame wasu da dama
Gwamnatin Tarayya ta yi aiki tare da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) don bankado ’yan Najeriya da suke tura kudade ga 'yan ta’addan Boko Haram.
Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa bayanan da ya gabatar a Channels ranar Talata sun yi daidai da yarjejeniyoyi tsakanin Najeriya da UAE.
Shehu ya ce a cikin wata sanarwa:
“Ana ta yada rahotanni marasa kyau da mummunan fassara, musamman a shafukan sada zumunta, bayan rahoton da ya fito a jaridar The Nation ta ranar Laraba game da murkushe masu daukar nauyin 'yan ta’adda da wannan gwamnatin ke yi.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirya kashe N396bn kan rigakafin Korona, Ministar Kudi
“Kowa ya sani cewa ainihin bayanin da na yi a gidan talabijin na Channels shi ne cewa bisa ga yarjejeniyoyi da ake da su, gwamnatin Najeriya ta yi aiki tare da UAE don tabbatar da bankado 'yan Najeriya a can kasar dake tura kudade ga ‘yan ta’addan Boko Haram.
"Hadaddiyar Daular Larabawa, kamar Najeriya, ba ta da wata ma'amala ta daukar nauyin 'yan ta'adda kuma tana aiki tare da kasar nan ta kowane fanni."
Shehu ya ce akwai shaidu da ke nuna cewa ana tura kudi daga Hadaddiyar Daular Larabawa ga shugabannin kungiyar ta Boko Haram.
Ya ce an kame mutane da yawa kuma bayan an gudanar da bincike, za a bankado wadanda ke da hannu a lamarin.
KU KARANTA: Babu wanda ya dauki Buhari da muhimmanci, hatta shugabannin hafsun soji, wani sanata
A wani labarin, Akalla mutane takwas ne suka mutu, wasu hudu kuma suka ji rauni sakamakon wasu ‘yan bindiga da suka kai hare-hare daban-daban a kan kananan hukumomin Chikun, Giwa da Kajuru na jihar Kaduna, Daily Nagerian ta ruwaito.
Samuel Aruwan, kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, ya bayyana abubuwan da suka faru a rahotannin da hukumomin tsaro suka gabatarwa gwamnati.
"A Kan Hawa Zankoro, kusa da Unguwan Yako a karamar hukumar Chikun, wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun harbi wata mota, daga nan kuma sai ta tarwatse, ta kai ga mutuwar mutane shida, sannan wasu hudu suka ji rauni," in ji shi.
Asali: Legit.ng