Gobarar kasuwar Katsina: An tara gudunmawar N170m zuwa yanzu, in ji gwamna Masari
- Kungiyar dattawan jihar Katsina sun kai wa gwamna Masari na jihar ziyarar jajantawa ranar Laraba
- Kungiyar ta jajantawa gwamnan da daukacin al'ummar jihar da iftila'in gobara ta makon da ya gabata
- Gwamna Masari ya bayyana adadin kudade da aka tara daga 'yan Najeriya a matsayin gudunmawa
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce kawo yanzu an tara zunzurutun kudi har Naira miliyan 170 daga masu hannu da shuni da sauran ‘yan Najeriya mutanen kirki, a matsayin gudummawa ga wadanda iftila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina.
Masari ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar dattawan Katsina karkashin jagorancin shugabanta, Ahmad Muhammad-Daku a gidan gwamnatin Katsina, ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.
"Kodayake har yanzu ba mu bude kofofin don ba da gudummawa ga wadanda bala'in gobarar ya shafa ba, mun kaddamar da kwamiti don gano musabbabin tashin gobarar", in ji shi.
KU KARANTA: Lauya ya nemi kotu ta yankewa Zakzaky da matarsa hukunci daidai da laifinsu
Gwamnan ya fadawa dattawan cewa kayayyaki masu yawa sun lalace, ciki har da kayan abinci da kayan kwalliya a gobarar.
Gwamna Masari ya yi godiya ga dattawan da suka samu lokaci domin yi masa, 'yan kasuwa, da daukacin mutanen jihar jaje kan gobarar.
Tun da farko, Shugaban kungiyar, Mista Daku ya bayyana cewa sun je gidan gwamnatin ne don jajantawa wa gwamnan da daukacin mutanen jihar.
Kungiyar ta yaba wa gwamnan kan nuna damuwa da jajircewa wajen shawo kan lamarin, tare da kafa kwamitin bincike don gano musabbabin tashin gobarar.
Sun roki Allah Madaukakin Sarki da ya kawo tallafi ga wadanda gobarar ta salwantar da dukiyoyinsu.
KU KARANTA: Zulum ya yiwa 'yan gudun hijira a Munguno goma na arzika
A wani labarin, Ahmad Babba Kaita, sanata mai wakiltar gundumar Katsina ta Tsakiya, ya jajantawa wadanda gobarar da ta lakume wasu sassan babbar kasuwar birnin ta shafa.
Daily Trust ta rahoto cewa, ya ba da gudummawar Naira miliyan 20 don ragewa 'yan kasuwar da abin ya shafa asara.
Ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar a ranar Asabar. A nasa martanin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Abbas Labaran Albaba, ya jinjinawa sanatan kan wannan karamci, da kuma duk sauran masu jajantawaa da ke zuwa rukuni-rukuni da kuma daidaiku don ba da gudunmawarsu.
Asali: Legit.ng