Sanatan Katsina ya tallafawa 'yan kasuwan da gobara ta shafa da N20m

Sanatan Katsina ya tallafawa 'yan kasuwan da gobara ta shafa da N20m

- Wani sanata daga jihar Katsina ya jajanta tare da taimakawa 'yan kasuwan da gobara ta shafa a Katsina

- Sanatan ya ziyarci kasuwar, ya kuma bada gudunmawar Naira miliyan 20 ga 'yan kasuwan

- Sarkin daura a wani bangaren, ya ziyarci kasuwar tare da nuna jimaminsa ga faruwar lamarin

Ahmad Babba Kaita, sanata mai wakiltar gundumar Katsina ta Tsakiya, ya jajantawa wadanda gobarar da ta lakume wasu sassan babbar kasuwar birnin ta shafa.

Daily Trust ta rahoto cewa, ya ba da gudummawar Naira miliyan 20 don ragewa 'yan kasuwar da abin ya shafa asara. Ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar a ranar Asabar.

A nasa martanin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Abbas Labaran Albaba, ya jinjinawa sanatan kan wannan karamci, da kuma duk sauran masu jajantawaa da ke zuwa rukuni-rukuni da kuma daidaiku don ba da gudunmawarsu.

KU KARANTA: Mutane 11 sun rasa rayukansu a hatsarin motan hanyar Bauchi da Kano

Sanatan Katsina ya tallafawa 'yan kasuwan da gobara ta shafa da N20m
Sanatan Katsina ya tallafawa 'yan kasuwan da gobara ta shafa da N20m Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani labarin makamancin wannan, mai martaba Sarkin Daura, Dr Umar Farouk Umar, shi ma ya kai ziyarar jajantawa ga Gwamnatin Jihar Katsina kan abin da ya faru.

Ya bukaci wadanda abin ya shafa su dauki abin da ya same su a matsayin wata jarabawa daga Allah kuma su yarda da shi da kyakkyawar niyya don samun cikakken sakamako.

Ya yi kira ga kungiyoyi da daidaikun mutane da su taimaka wa wadanda lamarin ya shafa, sannan ya gode wa Gwamna Aminu Bello Masari kan jajircewarsa wajen sake gina kasuwar.

KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai taba alkawarin mai da Naira daidai da dala ba

A wani labarin, A safiyar Litinin din nan ne gobara ta kama a babbar kasuwar Jihar Katsina, wadda aka fi sani da Central Market, rahotanni na cewa an yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira a yayin lamarin.

An gano cewa wutar ta fara ne misalin karfe 8 na safe. kuma ta ci gaba da lalata shagunan da ke kasuwar, yayin da wasu da gobarar bata shafa ba ‘suka dunguma suka kwashe kayansu kafin wutar da ta tashi ta isa shagunansu.

Wakilin jaridar This Day wanda ya ziyarci kasuwar ya ruwaito cewa ba a iya gano asalin abin da ya faru da kuma yadda gobarar ta faro ba a lokacin hada wannan rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.