Osinbajo ke jagorantar taron majalisar zartarwa bayan tafiyar Buhari Landan

Osinbajo ke jagorantar taron majalisar zartarwa bayan tafiyar Buhari Landan

- Mataimakin shugaban ƙasa frofesa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartar wa na yau bayan tafiyar Buhari Landan

- Majalisar zartarwar a taron ta na yau Laraba ta bada minti ɗaya na shiru don girmama tsofaffen ministocin da suka rasu a satin nan

- A wannan satin dai taron na majalisar zartarwa na gudana ba tare da shugaba Muhammadu Buhari ba kasancewar ya tafi Landan duba lafiyarsa

Mataimakin shugaban Ƙasa, Prof. Yemi Osinbajo, ke jagorantar taron majalisar zartarwa na yau bayan tafiyar shugaban Ƙasa Landan.

Majalisar zartarwa ta bada minti ɗaya na shiru don girmama tsofaffin ministoci, Sanata Bode Olowoporoku da kuma Alhaji Umaru Muhammad Baba.

KARANTA ANAN: Shugaban kasa ya bada izinin ayi nade-dade a aikin Gwamnati kafin ya tafi Ingila

Ya yin da yake sanar da mutuwar tsoffin Ministocin biyu, Sakataren gwamnatin tarayya, Mr Boss Mustapha, ya haƙalto wasu ayyukan da suka yi ma ƙasa.

Senator Olowoporoku, wanda ya wakilci mazaɓar Ekiti ta kudu, ya riƙe muƙamin ministan kimiyya da fasaha a jamhuriya ta biyu, The Nation ta ruwaito.

Ya rasu a ranar Laraba 24, ga watan Maris yana da shekaru 76 a duniya.

Alhaji Umaru Muhammad Baba ya riƙe muƙamin minista sau biyu, ministan albarkatun man fetur da kuma ministan tsaron cikin gida.

Yanzu-Yanzu: Osinbanjo ke jagorantar Taron majalisar zartarwa bayan tafiyar Buhari Landan
Yanzu-Yanzu: Osinbanjo ke jagorantar Taron majalisar zartarwa bayan tafiyar Buhari Landan Hoto: @ChannelsTv
Source: Twitter

Ya rasu a ranar Jumu'a 26, ga watan Maris yana da shekaru 81 a duniya.

KARANTA ANAN: 2023: Takarar Tinubu ta samu gagarumin goyon baya daga gwamnonin arewa da masu ruwa da tsaki

Daga cikin waɗanda suka halarci taron majalisar zartarwa na yau akwai: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Frofesa Ibrahim Gambari da mai bada shawara ta musamman kan harkar tsaro, Mejo janar Babagana Monguno.

Daga cikin ministocin da suka halarta akwai: ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ministan wutar lantarki, Mamman Saleh, ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammad, da kuma ministar kuɗi da tsare-tsare, Mrs Zainab Ahmed.

Sauran sun haɗa da: Ministan birnin tarayya, Muhammed Bello, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, da kuma Alƙalin alƙalai kuma ministan shari'a, Abubakar malami.

A wani labarin Kuma Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta

Hajiya Hadiza Elrufa'i ta ce tun kafin ta fito mijin nata ya gargaɗe ta da cewa ba zai biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa idan aka sace ta

Har yanzun dai ɗalibai 39 na hannun yan bindiga, kuma sun nemi a biya su 500 miliyan kafin su sake su.

Source: Legit

Online view pixel