Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta

Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta

-Uwar gidan gwamnan Kaduna takai ziyara gonar ta inda ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ba zata biya kuɗin fansa ba

- Hajiya Hadiza Elrufa'i ta ce tun kafin ta fito mijin nata ya gargaɗe ta da cewa ba zai biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa idan aka sace ta

- Har yanzun dai ɗalibai 39 na hannun yan bindiga, kuma sun nemi a biya su 500 miliyan kafin su sake su

Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza malam Nasir Elrufa'i ta kai ziyara gonar ta, ta kuma ce mijinta ya faɗa mata ba maganar biyan kuɗin fansa idan aka sace ni.

KARANTA ANAN: 'Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia

Hadiza El-rufa'i, matar gwamnan Kaduna Malam Nasiru Elrufa'i, ta ce mijinta ya faɗa mata cewa ba bu wasu kuɗin fansa da za'a biya idan aka sace ta.

Hadiza ta yi amfani da kafar sada zumunta ta tuwita wajen turo hotunan ta a cikin gonar ta, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta
Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta Hoto: @hadizel
Asali: Twitter

A jawaban da ta yi, ya yin turo hotunan a kafar sada zumunta, matar gwamnan ta tabbatar da cewa mijin nata ya gargaɗe ta a kan kar taje gonar.

Duk da cewa matar gwamnan bata yi amfani da kalmar 'Sace mutum' ko 'Kuɗin fansa' ba amma mutum zai iya gane inda maganar ta dosa.

Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta
Uwar Gidan El-rufa'i taje duba gonarta, ta ce Mijinta bazai biya kuɗi ba idan aka sace ta Hoto: @hadizel
Asali: Twitter

Bayan ta turo hotunan, Hadiza ta ce:

"Gani a gonata, duk wanda ke tunanina to ya daina. Mijina ya riga da ya gargaɗe ni da cewa bazai biya ko sisi ba."

KARANTA ANAN: Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriyar Burtaniya

Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da yan bindiga ke yawan kai hari su sace mutane don biyan su kiɗin fansa.

Jaridar Dailytrust ta kawo rahoton yadda aka sace 39 a makarantar koyon zamanatar da gandun daji dake Afaka, ƙaramar hukumar Igabi.

Tun bayan faruwar hakan a farkon watan Maris, gwamnatin jihar ta jaddada aniyarta na bazata biya kuɗi a saki kowa ba.

Amma waɗanda suka sace ɗaliban sun nemi a biya 500 miliyan kafin su sake su.

Haka zalika, a cikin satin nan aka sace mambobin ƙungiyar kiristoci RCCG a jihar dai ta Kaduna, dake arewa maso yammacin Najeriya.

A wani labarin kuma Sanatoci sun ba Gwamnan CBN, Emefiele kwana 3 ya zo gabansu a kan zargin bacewar Biliyan 4

A ranar Litinin ne majalisar dattawan Najeriya ta ba gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, wa’adin sa’o’i 72 domin ya bayyana a gabanta.

‘Yan majalisar su na neman Godwin Emefiele ne kan zargin bacewar Dala miliyan 9.5 daga asusun Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262