2023: Takarar Tinubu ta samu gagarumin goyon baya daga gwamnonin arewa da masu ruwa da tsaki
- Shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na iya samun tikitin jam’iyyar gabanin takarar shugaban kasa a 2023
- Akwai alamu da ke nuna cewa tsohon gwamnan na jihar ta Legas na samun goyon bayan manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar
- An ce Tinubu ya samu goyon bayan gwamnonin arewa uku da wasu jiga-jigan jam'iyyar a arewa
Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa ya nuna cewa takarar shugaban kasa na tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ta samu gagarumar karbuwa a 'yan makonnin da suka gabata.
A cewar rahoton, manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) suna ta bayyana goyon bayansu ga Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi yunkurin juyin mulki a Nijar, amma ba a yi nasara ba
Muhimmin abu ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, gwamnonin arewa da dama sun nuna goyon baya ga kudirinsa.
Tun da farko dama dai, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano bai boye goyon bayan sa ga Tinubu ba yayin da aka shirya wa tsohon gwamnan na jihar Lagas liyafa a jihar ta arewa maso yamma kwanan nan, inda aka gabatar da laccar ranar haihuwar.
Majiyoyin da aka ruwaito a cikin rahoton sun kuma nuna cewa kudirin Tinubu ya samu goyon bayan Aminu Bello Masari, gwamnan Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaya a Majalisar Dattawa kuma jigo a Jam’iyyar APC daga jihar Katsina, Sanata Abu Ibrahim, ya nuna goyon bayansa ga Tinubu a lokacin kaddamar da kungiyar Bola Tinubu Support Organisation a Abuja.
Hakazalika, wani tsohon Sakataren gwamnatin jihar Neja, wanda ya jagoranci bikin kaddamar da kungiyar, Farfesa Mohammed Kuta Yahaya, ya bukaci ‘yan Najeriya da su mara wa Tinubu baya.
KU KARANTA KUMA: Najeriya fa na cikin mawuyacin hali, matsaloli ta ko ina: Jadakar Birtaniya
Mabiya sun kuma nuna cewa kudirin na Tinubu zai samu kyakkyawar goyon baya daga gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, wanda a kwanan nan ya ayyana cewa ya zama dole a mika mulki ga Kudu don amfanin daidaito da adalci.
A wani labarin, mun ji cewa canjin suna a shafin Wikipedia na Bola Tinubu ya tayar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 69 a ranar Litinin, 29 ga Maris.
'Yan siyasa da shugabannin Najeriya sun taya shi murna matuka a shafukan sada zumunta.
Asali: Legit.ng