Shugaban kasa ya bada izinin ayi nade-dade a aikin Gwamnati kafin ya tafi Ingila

Shugaban kasa ya bada izinin ayi nade-dade a aikin Gwamnati kafin ya tafi Ingila

- Za a fara shirin nada sababbin sakataron din-din-din a Gwamnatin Tarayya

- Dr. Folashade Yemi-Esan ta bayyana wannan a wata takarda a ranar Talata

- Shugaban kasa ya amince a maye gurbin sakatarorin da su ka yi ritaya a 2021

Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sababbin sakatarorin din-din-din a ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Wannan sanarwa ta zo ne cikin wani jawabi da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr. Folashade Yemi-Esan ta fitar a Abuja.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa Dr. Folashade Yemi-Esan ta bayyana cewa za a maye guraben wasu sakatarorin da su ka bar aiki.

KU KARANTA: Abin da aka gano game da Boko Haram da ‘Yan bindiga ya na da ban-tsoro

Yemi-Esan ta ce sakatarorin din-din-din da su ka yi ritaya a shekarar nan sun fito ne daga jihohin Ekiti, Enugu, Katsina, Legas da Nasarawa.

Shugaban Muhammadu Buhari ya bada dama a fara shirye-shiryen zakulo wasu sababbin sakatarorin.

Shugaban ma’aikatan gwamnatin kasar ta ce za a cike guraben ne da jami’an gwamnatin da su ka kai matsayin darekta a mataki na 17 a 2019.

Ma’aikacin gwamnatin tarayya da ya zama darekta a ranar 1 ga watan Junairu, 2019 ko kafin nan ne kadai za ayi la’akari da shi wajen zabin.

Shugaban kasa ya bada izinin ayi nade-dade a aikin Gwamnati kafin ya tafi Ingila
Dr. Folashade Yemi-Esan a fadar Aso Villa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yunkurin gwamnati na rufe layuka marasa NIN ya gamu da cikas

Bayan haka ma’aikatan da su ka fito daga wadannan jihohi, kuma su ka cika bayanansu a shafin IPPIS, za su iya neman wadannan mukamai.

Yemi-Esan ta bukaci sakataron din-din-din masu-ci, su aiko mata da sunayen darektocin da su ke kan matakin aiki na 17 a ma’aikatunsa.

An umarci sakatarorin su aiko da duk wasu bayanan wadannan ma’aikata da kuma takardu na 20 na neman aikinsu watau Curriculum Vitae.

A farkon makon nan kun ji cewa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin darektoci a Ma’aikatar NASENI.

Dr. Olayinka Adunni Komolafe ta zama sabuwar Darektar hukumar NASENI. Ana sa ran ita da sauran darektocin hudu za su sauka a 2026.

Asali: Legit.ng

Online view pixel