'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

- 'Yan bindiga sun sake kai hari a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

- Yayin harin mabanbanta da suka kai, yan bindigan sun kashe mutane tara a Ungwan Jere da Ungwan Maje

- Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi bakin cikin afkuwar lamarin sannan ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu

'Yan bindiga a jihar Kaduna sun kashe manoma ta guda tara a hare-hare mabanbanta da suka kai a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a jihar.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, a ranar Alhamis, ya ce yan bindigan sun tare hanyar Dogon Dawa-Kuyello, bayan kauyen Ungwan Jere da ke karamar hukumar Birnin Gwari suka bindige mutum shida.

'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna
'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: 'Yan Hisbah Sun Kai Samame Gidan Ɗaliban Jami'a, Sun Kama Mace da Namiji a Ɗaki Ɗaya

Mutanen da suka kashe sune: Nura Rufai, Sanusi Gajere, Yakubu Labbo, Usman Dangiwa, Alhaji Abdulhamid da Junaidu Tsalhatu.

Kazalika, a Ungwan Maje da ke karamar hukumar Birnin Gwari, yan bindigan sun bindige wasu mutum biyu har lahira, sune Haruna Dotu da Hamisu Mohammad.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

Yan bindigan kuma sun kai hari kauyen Kwama da ke karamar hukumar Giwa sun kashe wani Nasiru Rufai, bayan ya ki yarda suyi garkuwa da shi.

Gwamna Nasiru El-Rufai ya yi bakin cikin samun labarin hare-haren ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma bawa iyalansu hakurin jure rashi.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164