Yanzu Yanzu: An yi yunkurin juyin mulki a Nijar, amma ba a yi nasara ba
- Labari da muka samu ya nuna cewa an yi kokarin juyin mulki a kasar Nijar
- An tattaro cewa an jiyo karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar da ke Yamai
- Sai dai kuma ba a cimma nasarar aikata hakan ba
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an yi yunkurin juyin mulki a Jumhuriyar Nijar, sai dai kuma ba a cimma nasarar hakan ba.
Shashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa an jiyo karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar Shugaban kasar da ke birnin Yamai.
KU KARANTA KUMA: Hadimin Buhari ya fara fallasa masu daurewa Boko Haram da Miyagun ‘Yan bindiga gindi
An kuma tattaro cewa wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje dake birnin na Yamai sun yi kira ga ma'aikatansu da su zauna a gida.
Sai dai kuma gidan rediyon kasar mallakar gwamnati dake birnin na Yamai na ci gaba da watsa shirye shiryensa ba tare da wata matsala ba.
A wani labarin, mun ji cewa jirgin Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ta isa birnin Landan da ke kasar Birtaniya inda zai ga likitocinsa kamar yadda hadiminsa @bashirahmaad ya sanar a Twitter.
A ranar Laraba 30 ga watan Maris ne shugaban na Nigeria ya baro birnin tarayya Abuja domin zuwa kasar Birtaniya.
Kafin zuwansa, shugaban kasar ya gana da manyan hafsoshin sojojin kasar inda ya zaburar da su da su gaggauta wurin kawar da bata gari da yan bindiga da ke adabar kasar.
Asali: Legit.ng