'Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia

'Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia

- ‘Yan Najeriya sun lura da sauyi kwatsam a cikin shekarun shugaban jam’iyyar APC na kasa a shafinsa na Wikipedia

- Daga hotunan da suka bayyana a kafafen sada zumunta, shekarun Tinubu sun sauka daga 79 zuwa 69 yayin da yake bikin cikarsa shekaru 69

- 'Yan Najeriya da dama na ganin akwai lauje a cikin nadi, wasu kuma sun ce hakan ya dasa alamomin tambaya kan sahihancin shekarunsa da aka yi biki a kai

Canjin suna a shafin Wikipedia na Bola Tinubu ya tayar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 69 a ranar Litinin, 29 ga Maris.

'Yan siyasa da shugabannin Najeriya sun taya shi murna matuka a shafukan sada zumunta.

KU KARANTA KUMA: Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan

'Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia
'Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia Hoto: @oreke_lewa, @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Wani mai amfani da shafin Twitter @_PLICE ne ya fara lura da bambancin shekarun bayan gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya aika sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga Tinubu a Twitter.

Mintuna kadan bayan ya ja hankali, sai wani mai amfani da shafin Twitter @oreke_lewa ya nuna cewa an gyara shekarun. Ya sauka daga 79 zuwa 69.

'Yan Najeriya sun rarrabu a tsakaninsu kan wannene ya kasance shekarunsa na hakika. Wasu na ganin cewa ya girmi shekaru 69.

@Danee_nk ya ce:

"Don haka, a cewarsu, Tinubu ya girmi SanwoOlu da shekaru 13 ne kawai. Lol."

@IhedibaMoses yayi sharhi:

"Wannan na fada muku ne cewa wadancan mutanen da ke kan mulki suna aiki tukuru a kan abin da ke faruwa a shafukan sada zumunta. A kaikaice mu ne muke cinsu gyara wanda su kuma suke aiwatarwa ..."

@kochdigit ya ce:

''A'a "Babu wanda zai iya canja abun da ya shafi wiki kuma ya bayyana a bainar jama'a. Ana gyare-gyare, amma wanda aka tabbatar kawai ake nunawa jama'a."

An san Wikipedia da ɗaukar tabbatacce kuma ingantaccen bayani daga tushe mai asali .

Duk da cewa abu ne mai sauki ga kowa yayi amfani da shi, Wikipedia ta ce ana tabbatar da bayanai, ciki harda na mashahurai da masu fada a ji daga tushe mai asali kafin jama'a su same shi.

Ba a san yadda aka yi Wikipedia ta yi irin wannan kuskuren ba a shekarun sanannen mutum da kuma dalilin da yasa ta gyara shi a ranar zagayowar haihuwarsa.

A gefe guda, makon nan ne ake bikin taya fitaccen ‘dan siyasar kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 69 da haihuwa.

Shehu Sani ya shiga rukunin wadanda su ka aika wa babban jagoran na APC mai mulki sakon taya murna a ranar Litinin, 29 ga watan Maris, 2021.

Dan siyasar ya ba tsohon gwamnan na jihar Legas shawarar ya dauki hayar tafinta a garin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel