Najeriya fa na cikin mawuyacin hali, matsaloli ta ko ina: Jakadar Birtaniya
- Najeriya na fama da mawuyacin matsalar tsaro a dukkan yankunanta shida
- Ministan tsaron Birtaniya ya kawo ziyara na musamman Najeriya
- Gwamnatin Birtaniya ta bayyana yadda take taimakawa wajen yiwa sojin Najeriya horo
Jakadar kasar Birtaniya, Catriona Laing, ta bayyana damuwarta kan tabarbarewar matsalar tsaro a Najeriya.
Yayin hira da manema labarai a bikin maraba da daliban Chevening da suka dawo gida, Catriona Laing, ta ce Birtaniya na iyakan kokarinta wajen taimakawa Najeriya wajen dakile matsalar tsaro, rahoton TheCable.
Ta ce Birtaniya da ta kasance tana taimakawa Sojojin Najeriya wajen horo, shirye-shirye, da kuma yadda ake cire bama-bamai.
"Gaskiya muna matukar damuwa da yadda lamarin tsaro ya tabarbare," Laing tace.
"Ku duba fa Najeriya na fuskantar matsaloli ta ko ina - a Arewa maso gabas, ta'addanci; a Arewa maso yamma, tsageranci, garkuwa da mutane; a Arewa maso tsakiya, rikicin makiyaya da manoma; a kudu rikicin yan Neja Delta."
"A kudu maso gabas kuwa, masu barazanar ballewa daga Najeriya. Saboda haka Najeriya na cikin mawuyacin hali."
"Muna na nan don taimako. Muna da sojoji a nan, wadanda suka zo bayan da aka sace daliban Chibok. Har yanzu muna baiwa Sojojin Najeriya horo, taimaka musu wajen shirye-shirye da kuma kawar da bama-bamai."
Ta kara da cewa makon nan Ministan tsaron Birtaniya ya kawo ziyara Najeriya don jaddada goyon bayan gwamnatin Birtaniya.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Faston Cocin Katolika Da Mai Girkinsa a kADUNA
DUBA NAN: Muna kan bakanmu, ba zamu taba yarda a sa Hijabi a makarantunmu ba, Cocin Katolika
A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin hafsoshin tsaro da sauran jami'an tsaro da na leken asiri da su gano tare da fitar da 'yan fashi, masu satar mutane da masu daukar nauyinsu.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno, ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa.
Ya fadi hakan ne bayan taron tsaro, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta a fadar gwamnatin, Abuja.
Asali: Legit.ng