Idan Najeriya ta tarwatse, dole kuyi Visa domin shiga Kano, in ji Osinbajo ga 'yan kudu

Idan Najeriya ta tarwatse, dole kuyi Visa domin shiga Kano, in ji Osinbajo ga 'yan kudu

- Mataimakin shugaban kasa ya nemi masu kira ga wargajewar kasar da su sake tunani

- Osinbajo yayi wannan kiran yayin gabatar da jawabin sa a taron tattaunawa na 12 na Bola Tinubu

- Hakazalika Osinbajo ya yabawa jihar Kano saboda kasancewarta gida ga masu son cigaba

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shawarci masu kira ga raba Najeriya da su sake tunani, ya kara da cewa idan Najeriya ta wargaje, dole su bukaci katin biza domin tafiya sassan arewa kamar Kano.

Osinbajo ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron tattaunawa na 12 na bikin cika shekaru 69 na Bola Tinubu da aka gudanar a jihar Kano, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Wasu tsiraru ba su isa su ayyana raba mu da Najeriya ba, in Akeredolu

Idan Najeriya tarwatse, dole kuyi Visa domin shiga Kano, in ji Osinbajo
Idan Najeriya tarwatse, dole kuyi Visa domin shiga Kano, in ji Osinbajo Hoto: worldstagegroup.com
Source: UGC

Mataimakin Shugaban kasar, wanda shine babban bako na musamman, ya ce taron a farko an shirya gudanar dashi ne ta yanar gizo, amma Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya dauki nauyin taron a zahiri wanda kuma zai gudana ta manhajar Zoom.

“Ga masu son ballewa zuwa kananan abubuwa, zuwa kananan kasashe, ya kamata a tuna musu cewa da ba za mu iya karbar tayin Gwamna Ganduje na zuwa Kano a takaitaccen lokaci ba tunda duk da za mu bukaci Visa don zuwa Kano,” in ji Osinbajo.

Osinbajo ya kara da cewa Kano waje ne mai matukar muhimmanci domin nan ne gidan masu akida ta ci gaban kasa.

KU ARANTA: Ku cire mu a jerin masu son ballewa daga Najeriya, jihohin Kudu ga masu son kafa Biafra

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a ranar Litinin ya ce dangane da batun hadewar kasa, dole ne duk ‘yan Najeriya su koma ga Allah.

Ganduje ya bayyana haka ne a jawabinsa na maraba a taro na 12 na zagayowar ranar haihuwar Bola Tinubu da ya gudana a jihar Kano.

Taron tattaunawar, wanda aka shirya don bikin cika shekara 69 na Tinubu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, an masa taken: “Hadin kan mu, arzikin mu: Wajibi ne ga hadin kan kasa don girma da ci gaba”.

Source: Legit.ng

Online view pixel