Marwa da wasu jami'an NDLEA sunyi gwajin ba-zata na shan miyagun kwayoyi

Marwa da wasu jami'an NDLEA sunyi gwajin ba-zata na shan miyagun kwayoyi

- Hukumar NDLEA ta gudanar da gwajin shan miyagun kwayoyi na ba-zata ga mambobin ta

- Hukumar ta fara da cikin gidanta ne don fita daga zargin da al'umma kan iya jefa ta nan gaba

- Hukumar ta bayyana gwajin a matsayin wani yunkuri na tsarkake dukkan wani lungu da sako na hukumar

Shugaban Hukumar hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Brig-Gen. Mohamed Buba Marwa (Mai ritaya) tare da Daraktoci da wasu jami’ai a hedkwatar hukumar ta kasa da ke Abuja a ranar Litinin sun mika kansu ga gwajin shan miyagun kwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar, Mista Femi Babafemi, ya ce an yiwa jami’an ba-zata ne lokacin da suka iso wurin aiki, an ba da umarnin rufe kofofin ofishin hedkwatar sannan kuma aka nemi dukkansu su taru a dakin taron hedikwatar.

A cewarsa, a zauren an gayyaci tawagar likitocin da ke karkashin jagorancin Daraktan lafiya na Synapse Services, Dokta Vincent Udenze, wani kwararre a ilimin tabin hankali, da aka riga aka gayyata tare da kayan aikinsu don gwajin ta hanyar daukar samfutrin fitsari.

KU KARANTA: Idan Najeriya ta tarwatse, dole kuyi Visa domin shiga Kano, in ji Osinbajo ga 'yan kudu

Marwa da wasu jami'an NDLEA sunyi gwajin ba-zata na shan miyagun kwayoyi
Marwa da wasu jami'an NDLEA sunyi gwajin ba-zata na shan miyagun kwayoyi Hoto: newsdiaryonline.com
Asali: UGC

A wani takaitaccen bayani jim kadan kafin ya fara nasa gwajin, Janar Marwa ya ce gwajin na ba-zata ya zama dole don tabbatar da cewa aikin ya fara daga cikin gida, Daily Trust ta ruwaito.

“Ba za mu iya sanya wasu su yi gwajin shan miyagun kwayoyi ba tare da mika kanmu ga irin hakan ba.

Ya bayyana matakin a matsayin mafari don tabbatar da hukumar ta kubuta daga mambobi masu shan miyagun kwayoyi don tunkarar sauran al'umma.

Marwa ya kara da cewa, "Babban abin da ya sa aka yi gwajin na ba-zata tare da gayyato ma'aikatan lafiya na waje don gudanar da gwajin shi ne kara karfafa ingancin aikin,” in ji shi.

Sakamakon gwajin da tuni likitocin suka fitar ya nuna cewa Janar Marwa tare da Sakataren Hukumar, Barista Shadrack Haruna da sauran Daraktoci a hedkwatar hukumar ta NDLEA duka sun tabbata basa shan kwayoyi.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje: Wajibi ne 'yan Najeriya su koma ga Allah

A wani labarin daban, Hukumar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kwamushe wani tsoho dan shekara 70 da ake zargi dai kai wa 'yan bindiga da 'yan Boko Haram miyagun kwayoyi.

NDLEA ta ce tsohon na zuwa ne daga jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar inda daga nan yake shigo da kwayoyin cikin kasar ta Najeriya.

Cikin wata sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce, tsohon mai suna Muhammad Rabi'u Wada da ke kai wa Boko Haram da 'yan bindiga kwaya an kame shi ne a jihar Neja kan hanyarsa ta komawa Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel