Yan Sanda sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Abuja, sun kwato makamai

Yan Sanda sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Abuja, sun kwato makamai

- Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta sami nasarar cafke wasu mutane da ake zargin masu satar mutane ne a Abuja

- Hukumar ta ƙwato makamai a hannun waɗanda ake zargin da suka haɗa da Bindigu da kuma babur ɗin hawa.

- Mai magana da yawun hukumar ta bayyana cewa binciken su bazai tsaya nan ba har sai sun raba Abuja da dukkan wani ta'addanci

Hukumar yan sanda a Abuja ta kama wasu mutane biyar a Kuje da Daki-biu waɗanda ake zargin suna da hannu a satar mutane a ƙauyen Kiyi, Abuja.

KARANTA ANAN: 'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa

An kama waɗanda ake zaginne tsakanin ranar Jumu'a 26 zuwa Lahadi 28 ga watan Maris ya yin wani sintiri da jami'an yan sanda daga ofishin dawaki suka yi Atare da taimakon jami'ai masu yaƙi da satar Mutane.

Waɗanda aka samu nasarar cafkewa sun haɗa da: Abdullahi Haruna, Haruna Musa, Iliyasu Adamu, Micheal Paul da kuma Salisu Abdullahi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Waɗanda aka kama ɗin sun shaida cewa suna bada masaniya ga yan fashin dake sace mutane a kauyen Kiyi.

Yan Sanda sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kwato makamai a Abuja
Yan Sanda sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kwato makamai a Abuja Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

Yan sandan sun kuma ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda biyu, da kuma babur ɗin bajaj guda ɗaya daga hannun mutanen.

KARANTA ANAN: Bukola Saraki ya kawo shawarwarin yadda PDP za ta ja hankalin ‘yan kasa da shekara 35 a 2023

Mai magana da yawun yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ASP Yusuf Mariam, ta bayyana cewa suna cigaba da ƙoƙarin kamo wasu gungun yan ta'addan.

Ta kuma ƙara da cewa: "Dukkan waɗanda ake zargi za'a gurfanar dasu a gaban ƙuliya da zaran an gama bincike."

Saboda haka hukumar 'yan sanda na rokon mazauna yankin da su kwantar da hankullansu ya yin da jami'an su zasu cigaba da bincike don zaƙulo duk wasu yan ta'adda, da kare rayuwar mazauna garin na Abuja.

A wani labarin kuma Sanatan Katsina ya tallafawa 'yan kasuwan da gobara ta shafa da N20m

Ahmad Babba Kaita, sanata mai wakiltar gundumar Katsina ta Tsakiya, ya jajantawa wadanda gobarar da ta lakume wasu sassan babbar kasuwar birnin ta shafa.

Sanatan ya ziyarci kasuwar, ya kuma bada gudunmawar Naira miliyan 20 ga 'yan kasuwan.

Source: Legit.ng News

Online view pixel