'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa

'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa

- Yan bindiga sun halaka, Ishaya Sule, tsohon shugaban PDP na karamar hukumar Tafa a jihar Niger sun kuma sace matarsa

- Yan bindigan sun afka gidan dan siyasan ne a daren ranar Lahadi suka sare shi da adda sannan suka harbe shi da bindiga a kirji

- Ibrahim Mami Ijah, shugaban karamar hukumar Tafa, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce yana tattara bayanai

'Yan bindiga sun bindige tsohon shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Tafa ta jihar Niger, Ishaya Sule, sun kuma yi awon gaba da matarsa mai suna Rebecca.

Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa ya ce lamarin ya faru a daren ranar Lahadi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa
'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa. @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

Ya ce yan bindigan sun afka gidan mamacin da ke Bwari-Saba a karamar hukumar Tafa misalin karfe 1.22 na daren ranar Lahadi.

Ya ce yan bindigan da suka shigo garin ta cikin daji sun haura katangar gidan dan siyasan yayin da wasu daga cikinsu suka tsaya a wajen gidan.

Ya ce sun baele kofar shiga gidan suka wuce dakin marigayin suke bindige shi nan take.

"Sun sare shi da adda kafin daya daga cikinsu ya harbe shi a kirji, sun kuma yi awon gaba da matarsa bayan hakan," in ji shi.

KU KARANTA: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

Shugaban karamar hukumar Tafa, Ibrahim Mami Ijah, ya tabbatar da kashe tsohon shugban na PDP, inda ya ce yana tattara rahoton kan lamarin don ya aika wa kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta.

"Mun kasa barci daren jiya a lokacin da na samu rahoton cewa an kashe tsohon shugaban PDP an kuma sace matarsa," in ji shi.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Niger, SCP Wasiu Abiodun ya yi alkawarin zai bada bayani amma bai bayar ba a lokacin hada wannan rahoton.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: