Bukola Saraki ya kawo shawarwarin yadda PDP za ta ja hankalin ‘yan kasa da shekara 35 a 2023

Bukola Saraki ya kawo shawarwarin yadda PDP za ta ja hankalin ‘yan kasa da shekara 35 a 2023

- Kwamitin NRSC ya ba NWC shawarar a cirewa matasa nauyin sayen fam

- Bukola Saraki ya ce a bar wa ‘yan kasa da 35 ne kujerar shugaban matasa

- Saraki ya na sa ran hakan zai kara jawo matasa su shiga jam’iyyar ta PDP

Kwamitin sulhu da dabaru da jam’iyyar PDP ta kafa ta bada shawarwarin yadda za a jawo hankalin matasa domin su shiga cikin harkar siyasa.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa kwamitin NRSC wanda Dr. Bukola Saraki ya ke jagoranta, ya bada shawarar a cire wa matasa biyan kudin fam.

Bukola Saraki ya na so shugabannin jam’iyyar PDP su bada dama ga duk wani ‘dan kasa da shekara 35 ya huta da kudin fam idan zai nemi takara.

KU KARANTA: Obasanjo ya na goyon bayan takarar 'Matashi'Yahaya Bello a zaben 2023

Wannan shawara ya na cikin wata wasika mai shafi guda da Bukola Saraki ya rubuta, ya aika wa shugaban PDP na kasa, Uche Secondus a ranar Alhamis.

Kwamitin na tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki, ya nemi Secondus ya sanar da majalisar NEC ta yi wa dokokin PDP kwaskwarima a kan hakan.

Bugu da kari, Saraki ya nemi a wajabta cewa duk mai neman kujerar shugaban matasa na jam’iyyar PDP a kowane mataki ya zama ‘dan shekara 18 zuwa 35.

A cewar kwamitin NRSC, an dauki wannan matsaya ne bayan wani taro da aka yi da daukacin shugabannin matasa na jam’iyyar adawar daga jihohi 36.

KU KARANTA: Tinubu ya cika shekara 69, Buhari ya yi magana

Bukola Saraki ya kawo shawarwarin yadda PDP za ta ja hankalin ‘yan kasa da shekara 35 a 2023
Bukola Saraki a taron PDP
Source: Twitter

Daga cikin bukatun da matasan PDP su ka gabatar a taron da aka yi shi ne a bar masu kujerarsu, sannan a dauke masu nauyin kashe kudi wajen sayen fam.

Hakan na nufin idan wani matashi ya na neman kujerar shugaban kasa, ba zai biya N20m na sayen fam ba, zai biya N1m ne rak na sayen takardar sha’awar takara.

Dazu kun samu labari cewa akwai sabani a tsakanin manyan PDP game da yankin da za a ba takara a zaben 2023 bayan aikin kwamitin Bala Mohammed.

Kwamitin gwamna Mohammed ya nemi PDP ta yi fatali da tsarin kama-kama da ake yi tsakanin Arewa da Kudu, amma wasu ba su gamsu da wannan shawara ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel