Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da babbar kasuwar Katsina

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da babbar kasuwar Katsina

- Gobara ta barke a babbar kasuwar jihar Katsina wato Central Market da sanyin safiyar yau Litinin

- Rahotanni sun bayyana cewa, shaguna da yawa sun kone kurmus, yayin da ake kokarin kashe wutar

- Hukumomin tsaro da suka hada da 'yan sanda sun hallara domin tabbatar da kiyaye dukiyoyin jama'a

A safiyar Litinin din nan ne gobara ta kama a babbar kasuwar Jihar Katsina, wadda aka fi sani da Central Market, rahotanni na cewa an yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira a yayin lamarin.

An gano cewa wutar ta fara ne misalin karfe 8 na safe. kuma ta ci gaba da lalata shagunan da ke kasuwar, yayin da wasu da gobarar bata shafa ba ‘suka dunguma suka kwashe kayansu kafin wutar da ta tashi ta isa shagunansu.

KU KARANTA: 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da babbar kasuwar Katsina
Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da babbar kasuwar Katsina Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Wakilin jaridar This Day wanda ya ziyarci kasuwar ya ruwaito cewa ba a iya gano asalin abin da ya faru da kuma yadda gobarar ta faro ba a lokacin hada wannan rahoto.

Amma gamayyar jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Katsina, hukumar kashe gobara ta tarayya da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA) suna ta fafutukar kashe wutar.

Rundunar 'yan sanda na Najeriya, Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), da Jami'an Tsaro NSCDC duk sun hallara a wurin don kula da tsaro.

KU KARANTA: Ekiti ta bai wa makiyaya wa'adin makwanni 2 su yi rajista ko su tattara su bar jihar

A wani labarin daban, Gobara a ranar Lahadi ta kone a kalla shaguna 63 a kasuwar Tundun Wada da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An kyautata zaton wutan ta taso ne daga wani shagon siyar da kifi wutar shagon ke da tangarda.

Yayin ziyarar da ya kai wurin da abin ya faru, Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya jajantawa wadanda abin ya shafa ya ce su dauki abin a matsayin kaddara ne daga Allah.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel