Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai taba alkawarin mai da Naira daidai da dala ba

Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai taba alkawarin mai da Naira daidai da dala ba

- Fadar shugaban kasa a Najeriya ta karyata ikirarin Buhari na mai da Naira daidai da darajar dala

- Fadar ta shugaban kasa ta bayyana cewa, babu inda shugaban kasa ya fadi haka, lallai karyane

- Hakazalika ta kalubalanci duk wani da yake ganin yana da hujjar inda shugaban kasar ya fadi haka

Fadar Shugaban kasa ta ce babu wani lokaci da gwamnati mai ci ta yi alkawarin sanya Naira daya ta zama daidai da darajar dala daya.

Mista Femi Adesina, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarin, ya ce ikirarin da ke nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi irin wannan alkawarin, karya ne.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin

Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai taba alkawarin mai da Naira daidai da dala ba
Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai taba alkawarin mai da Naira daidai da dala ba Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

"Babu shi, bogi ne, karya ne, rudu ne, babu shi" Mista Adesina ya bayyana yayin wani shiri a matsayin bako na Talabijin din Channels wato Sunday Politics.

Adesina ya ce Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ya yi ikirarin karyata zancen sau da yawa kuma ya kalubalanci duk wanda ke da batun a bidiyo ko a wallafe-wallafe da ya bayyana su a matsayin hujja.

KU KARANTA: Ci gaba: Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakai da su nuna jagoranci na gari abin misalaltawa, domin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a wani sako da ya aika a laccar shekara-shekara ta 2021 da ake gabatarwa a gidan Arewa House da aka gudanar ranar Asabar a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel