Mutane 11 sun rasa rayukansu a hatsarin motan hanyar Bauchi da Kano

Mutane 11 sun rasa rayukansu a hatsarin motan hanyar Bauchi da Kano

- Hatsarin mota a hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 10 a daren Lahadi

- Hukmar FRSC ta tabbatar da afkuwar hatsarin, ta kuma shaidawa manema labarai lamarin

- Hakazalika wata mota a hanyar Kano zuwa Zariya ta kone kurmus, inda direbanta shi ma ya mutu

Akalla mutane 10 ne rahotanni suka bayyana mutuwarsu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kusa da garin Bara da ke cikin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Kodayake bayanai kan abinda ya faru ba su da yawa, amma wakilin jaridar Punch ya samu labarin cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 7 na daren ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban motar bas din da ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Gombe daga jihar Kaduna ya yi kokarin kauce wa rami amma sai ya rasa gane kan motar ya fada daji.

An ce daya daga cikin tayar motar ya fita kafin motar ta tarwatse.

KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai taba alkawarin mai da Naira daidai da dala ba

Mutane 11 sun rasa rayukansu a hatsarin hanyar Bauchi da Kano
Mutane 11 sun rasa rayukansu a hatsarin hanyar Bauchi da Kano Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa, reshen Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar hatsarin.

Abdullahi ya kara da cewa, "Da zaran aikin ceton ya kammala kuma na samu cikakkun bayanai game da hatsarin, zan tuntube ku dashi."

Hakazalika, direban motar Toyota Hiace bas mai lamba BKD 265 XA ya mutu ranar Lahadi a wani hatsarin mota shi kadai a hanyar Zariya zuwa Kano.

Direban mai shekaru 40, mai suna Abdullahi Haruna, ya mutu ne a lokacin da ya isa asibitin Murtala Muhammed dake Kano, inda aka garzaya da shi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, a cikin wata sanarwa ya ce an mika gawar direban ga ofishin ‘yan sanda na 'Yar Akwa bayan da likita ya tabbatar da mutuwarsa.

“Wani Abdul Danlami Jibrin, na hanyar Zariya ya kira jami’an kashe gobara da misalin karfe 10:07 na safe don sanar da ita hatsarin; mutanen hukumar sun isa wurin da misalin karfe 10:19 na safe,” in ji sanarwar.

KU KARANTA: Mazauna wani yankin Abuja sun fara barin gidajensu saboda sace mutane

A wani labarin daban, Karamar Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Mariam Katagum, a ranar Litinin ta ce tun daga farkon wadanda suka fara cin gajiyar shirin a ranar 17 ga Janairun 2021, an amince da biyan jimilar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin Survival Fund a fannin sufuri.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya fitar a wasu tarurruka da aka gudanar na shirin, jaridar Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Jimillar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin a fannin sufuri ya zuwa yanzu an amince da a biya su yayin da har yanzu mutum 9,109 ke jiran tantacewa don biya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel