Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci shugabanni a dukkan matakai da su zama jagorori na gari

- Shugaban ya kuma jaddada bukatarsa ga masu ruwa da tsaki wajen shawo kan matsalolin kasar

- A karshe ya jaddada burin gwamnatinsa na inganta tsaro, tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakai da su nuna jagoranci na gari abin misalaltawa, domin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a wani sako da ya aika a laccar shekara-shekara ta 2021 da ake gabatarwa a gidan Arewa House da aka gudanar ranar Asabar a Kaduna.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan sa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su fifita al’ummar kasar a gaba, a duk harkokin su, kamar yadda magabatan kasar suka yi, kamar su Sir Ahmadu Bello.

Ya jaddada cewa kyakkyawan shugabanci zai samar da wata kafa ga kasar don shawo kan kalubalenta da kuma bude manyan dama ga kasar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun kashe 'yan banga sama da 20 a jihar Neja

Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma
Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

"Ikonmu na hada karfi wajen tunkarar kalubale a cikin kasarmu a yau zai tafi tare ne wajen bude babbar damar da take da shi sannan kuma abin farawa shi ne jagoranci abin misaltawa," in ji shi.

Buhari ya kara da cewa akwai bukatar inganta daidaito da aiki tare a tsakanin shugabanni, domin samar da shugabanci na gari a matakin tarayya, na jihohi da na Kananan Hukumomi, a wani yunkuri na kai kasar ga tudun mun tsira.

“Bai kamata mu dauka cewa matsalolin kasarmu shugaba Buhari ne ya kamata kuma zai iya magance su shi kadai ba.

“Eh, muna jagoranci ne da misali, amma duk wani mai ruwa da tsaki yana da alhakin yin aiki tare da sanya bukatun kasarmu a gaba kuma mafi muhimmanci.

“Bai kamata mu manta da nagarta ta sadaukar da kai ba, wacce ta samo asali ga iyayenmu na kwarai, kamar su Sardauna.

Ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen jajircewarta na inganta tsaro, gina tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

KU KARANTA: Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari

A wani labarin daban, Tsohon shugaban gidauniyar kayan aikin 'yan sanda, Cif Kenny Martins a ranar Alhamis ya bayyana cewa biyo bayan karuwar rashin tsaro a kasar, 'yan Najeriya daban-daban na kashe sama da N1tn a duk shekara don samar wa kansu da dukiyoyinsu tsaro.

Martins ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron lakca karo na 4 na Kamfanin Sadarwa na BAT tare da taken: "Kalubalen Tsaro da Tasirinsa kan Ci gaban Kasa," wanda aka gudanar a Otal din Sheraton da ke Legas.

Ya bukaci gwamnati da ta taka rawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kasar, Nigeria Trubute ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel