Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano

Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano

- Shugaban jam'iyyar APC ya ziyarci jihar Kano, inda ya bayyana gudanar da bikin ranar haihuwarsa

- Shugaban na APC ya zarce zuwa kai ziyar ban girma zuwa fadar sarkin Kano, inda ya bayyana mubaya'arsa

- A cikin kasa da mako, shugaban na APC ya ziyarci manyan jihohi masu yawan kuri'u a arewacin Najeriya

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya isa jihar Kano duk da adawar da ake nunawa kan gudanar da bikin ranar haihuwarsa a jihar.

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) ta nemi Gwamna Abdullahi Ganduje da kar ya karbi bakuncin gudanar da bikin ranar haihuwar ta Tinubu a jihar.

Amma a ranar Lahadi, Ganduje ya raka Shugaban Jam’iyyar ta APC na kasa zuwa fadar mai martaba Sarkin Kano, inda ya yi masa mubaya’a.

KU KARANTA: Atiku: Domin ceton kanmu, dole ne mu taimakawa gwamnatin Buhari

Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano
Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano Hoto: thenationonline.net
Asali: UGC

A ranar Litinin ne ake sa ran Tinubu zai gana da Majalisar Sarakunan Gargajiyan Najeriya.

Akwai alamu da ke nuna cewa Tinubu ya zura wa kujerar shugaban kasa ido, duk da cewa bai fito fili ya bayyana aniyarsa ba.

Da yake jawabi a fadar, Tinubu ya yarda cewa kasar na cikin wani mawuyacin hali, yana mai cewa hadin kai da ci gaba ne kawai zai ba ta damar tsira.

"Najeriya tana cikin mawuyacin halin rayuwarta kuma abin da zai sa ta ci gaba shi ne hadin kai da fahimta, saboda haka, Legas da Kano, wadanda suka shaida irin wannan lokuta, dole ne su nuna hanya."

Da yake mayar da martani, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya yaba wa Tinubu kan zabar Kano da ya yi don bikin cikarsa shekara 69 da haihuwa, yana mai cewa wannan kadai shaida ce ga hadin kai da kaunar da yake da ita ga Najeriya.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin watanni hudu da Tinubu ya ziyarci jihar.

A cikin kasa da mako guda, Tinubu ya je Kaduna da Katsina, wadanda suna daga cikin jihohin da suka fi yawan masu jefa kuri’a a kasar.

KU KARANTA: NDLEA ta kame wani tsoho dan shekara 70 dake kaiwa 'yan Boko Haram kwaya

A wani labarin daban, Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a 2019 Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatin Buhari kan hanyoyin da za ta bi ta magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Atiku ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wani rahoto da Bloomberg ta fitar cewa Najeriya, itace kasa mafi yawan mutanen da ke fama da talauci a duniya, da alama kuma za ta sake karya wani tarihin na zama kasa mai mafi yawan marasa aikin yi a duniya.

Atiku, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter kuma jaridar Legit ta gano ya bayyana cewa, gwamnatin mai ci a Najeriya na bukatar taimako don ceto kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.