NDLEA ta kame wani tsoho dan shekara 70 dake kaiwa 'yan Boko Haram kwaya

NDLEA ta kame wani tsoho dan shekara 70 dake kaiwa 'yan Boko Haram kwaya

- Hukumar sNDLEA ta kame wani tsoho dake jigilar kai wa 'yan ta'adda a Najeriya muggan kwayoyi

- Hukumar ta kuma dira wata katafariyar gonar taba a wani yankin jihar Ondo a kudancin kasar

- Hakazalika ta samu nasarar kame wani bata-gari da harin taba a wani shingen ababen hawa a jihar Kogi

Hukumar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kwamushe wani tsoho dan shekara 70 da ake zargi dai kai wa 'yan bindiga da 'yan Boko Haram miyagun kwayoyi.

NDLEA ta ce tsohon na zuwa ne daga jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar inda daga nan yake shigo da kwayoyin cikin kasar ta Najeriya.

Cikin wata sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce, tsohon mai suna Muhammad Rabi'u Wada da ke kai wa Boko Haram da 'yan bindiga kwaya an kame shi ne a jihar Neja kan hanyarsa ta komawa Jamhuriyar Nijar.

KU KARANTA: Atiku: Domin ceton kanmu, dole ne mu taimakawa gwamnatin Buhari

NDLEA ta kame wani tsoho dan shekara 70 dake kaiwa 'yan Boko Haram kwaya
NDLEA ta kame wani tsoho dan shekara 70 dake kaiwa 'yan Boko Haram kwaya Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

A wani samame da hukumar ta kai mai kama da wannan, ta samu nasarar lalata gonar tabar wiwi a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya wadda girmanta ya kai kimanin hekta 95.

An samu gonar ne a wani dajin dake Ogbese, sai dai ba a samu nasarar kame kowa ba yayin samamen, amma ana ci gaba da bincike domin gano wanda ya mallaki gonar.

A jihar Kogi da ke arewacin kasar ta Najeriya, har ila yau Hukumar ta samu nasarar kwace tabar wiwi da ta kai kimanin kilogiram 116.1 a wani shingen ababan hawa a yankin Okene-Lokoja.

Mutumin da aka kama da kayan mai suna Sulaiman Said ya ce ya dauko tabar ta wiwi din ne daga jihar Edo a kudancin Najeriya kuma zai cilla da ita har zuwa Jihar Kaduna ne.

KU KARANTA: Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

A wani labarin daban, ‘Yan bindiga sun kashe 'yan banga sama da 20 a wani hari da suka kai Kotonkoro a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Harin kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Hausa ta ruwaito, ya faru ne a ranar Litinin bayan da 'yan banga suka yi arangama da wasu gungun 'yan bindiga a yankin.

Ibrahim Ilyasu, dan majalisar dokokin jihar daga Mariga, ya ce:

“A ranar Litinin, an yi artabu tsakanin 'yan banga da ’yan bindiga kuma suka bi su zuwa wani daji da ke kusa da su don su yake su. Abun takaici, an kashe 'yan banga kuma 'yan bindigan sun ki baiwa al'umma damar kwaso gawarwakinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel