Atiku ya bayyana Hanyoyi 3 da Buhari zai bi don magance matsalar rashin aikin yi

Atiku ya bayyana Hanyoyi 3 da Buhari zai bi don magance matsalar rashin aikin yi

- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin Buhari

- Ya lissafo wasu hanyoyi uku da gwamnatin ya kamata ta bi a magance matsalar rashin aikin yi

- Wasu 'yan Najeriya sun mayar da martani kan maganar tasa, wani na ganin duk kanwar ja ce

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a 2019 Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatin Buhari kan hanyoyin da za ta bi ta magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Atiku ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wani rahoto da Bloomberg ta fitar cewa Najeriya, itace kasa mafi yawan mutanen da ke fama da talauci a duniya, da alama kuma za ta sake karya wani tarihin na zama kasa mai mafi yawan marasa aikin yi a duniya.

Atiku, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter kuma jaridar Legit ta gano ya bayyana cewa, gwamnatin mai ci a Najeriya na bukatar taimako don ceto kasar baki daya.

Ya kuma danganta yawaitar aikata laifuka da rashin aikin yi da kasar ke fuskanta wanda ba a taba gani ba.

KU KARANTA: NDLEA ta kame wani tsoho dan shekara 70 dake kaiwa 'yan Boko Haram kwaya

Atiku ya bayyana Hanyoyi 3 da Buhari zai bi don magance matsalar rashin aikin yi
Atiku ya bayyana Hanyoyi 3 da Buhari zai bi don magance matsalar rashin aikin yi Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Saboda haka ya ba da shawarar wasu abubuwa uku don magance rashin aikin yi na matasa a kasar kamar haka:

1. Kowane ahali a Najeriya da ke da a kalla yaro daya dake zuwa makaranta, kuma yana samun kasa da $800 a kowace shekara ya kamata ya rika karbar N5,000 daga gwamnati a kowane wata ta hanyar BVN da NIN.

2. Sanya yara miliyan 13.5 da basa makaranta a fadin Najeriya a makarantu.

3. Sanya matasa wadanda suka wuce shekarun makaranta a cikin wani tsarin gwamnati na ayyukan jama'a.

Biyo bayan maganarsa, wasu 'yan Najeriya a kafar Twitter sun mai da martani, in da wani yUche, @UcheElias1 yake cewa:

"Duk daya suke, tabbas, amma ina tunanin cewa ya yi magana ne a matsayinsa na dan kasa mai nuna damuwarsa?"

moh'd Bashir lawal, @ bashor1010 ya ce:

"Yallabai, a gaskiya dukkanku shugabannin da suka gabata da na yanzu na kasar nan kun ba da gudummawa matuka ga wadannan matsalolin da muke ciki. Don Allah ku daina siyasantar da halin da ake ciki, kawai a samar da mafita ga matsalolin, abu mai sauki!"

KU KARANTA: Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

Satu Jatau Jewon, @JatauSatu ya ce:

"Babu kasar da za ta taba cimma burinta na samar da aikin yi idan har ba a samar da ita daga mataki na biyu na samar da kayayyaki ba.

"Najeriya ta kasance a matakin farko tun daga shekaru sittin kuma ta kara tabarbarewa. Haka nan tsarin da ke cike da rashawa mai girman gaske da muke gani a Najeriya ba zai taba iya kawo ci gaba ba."

A wani labarin kuwa, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na bukatar taimako, Daily Trust ta ruwaito.

Aiku Abubakar ya bayyana haka ne a cikin wata makala mai taken: ‘Matsakaicin rashin aikin yi mafi girma a Duniya: Lokaci Don Taimakawa Wannan Gwamnati ta Taimakawa Najeriya’.

Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 ya bayyana cewa, taimakawa wannan gwamnati mai ci shine mataki na ceton ilahirin 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.