Atiku: Domin ceton kanmu, dole ne mu taimakawa gwamnatin Buhari

Atiku: Domin ceton kanmu, dole ne mu taimakawa gwamnatin Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana bukatar taimakawa gwamnatin Buhari

- Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin ya kamata take daukar shawarwarin da 'yan Najeriya ke bayarwa

- Ya kuma bayyana rashin jin dadinsa ga yadda rashin aikin yi ya hau-hawa a fadin kasar zuwa wani kaso mai girma

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na bukatar taimako, Daily Trust ta ruwaito.

Aiku Abubakar ya bayyana haka ne a cikin wata makala mai taken: ‘Matsakaicin rashin aikin yi mafi girma a Duniya: Lokaci Don Taimakawa Wannan Gwamnati ta Taimakawa Najeriya’.

Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 ya bayyana cewa, taimakawa wannan gwamnati mai ci shine mataki na ceton ilahirin 'yan Najeriya.

KU KARANTA: Wasu tsiraru ba su isa su ayyana raba mu da Najeriya ba, in Akeredolu

Atiku: Domin ceton kanmu, dole ne mu taimakawa gwamnatin Buhari
Atiku: Domin ceton kanmu, dole ne mu taimakawa gwamnatin Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce maimakon sauraran shawarwari, gwamnatin tana karantar ma'anoni marasa kyau ga ra'ayoyi da shawarwarin da masu sukarta ke bayarwa.

Atiku ya kuma danganta yawaitar aikata laifuka da rashin aikin yi da kasar ke fuskanta wanda ba a taba gani ba.

“Ban taba jin bakin ciki sosai ba, kamar yadda naji yayin da naga rahoto daga Bloomberg Business a ranar Asabar, 27 ga Maris, 2021 cewa Najeriya za ta fito a matsayin kasar da ke kan gaba wajen yawan marasa aikin yi a duniya, a kan sama da 33%.

“Mun yi gargadi game da wannan, amma fadakarwar da da ni da wasu masu kishin kasa suka yi a banza. Gashi yanzu.

KU KARANTA: ‘Yan Najeriya na kashe sama da N1trn don kare kansu a duk shekara, in ji Kenny Martins

A wani labarin daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakai da su nuna jagoranci na gari abin misalaltawa, domin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a wani sako da ya aika a laccar shekara-shekara ta 2021 da ake gabatarwa a gidan Arewa House da aka gudanar ranar Asabar a Kaduna.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan sa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su fifita al’ummar kasar a gaba, a duk harkokin su, kamar yadda magabatan kasar suka yi, kamar su Sir Ahmadu Bello.

Asali: Legit.ng

Online view pixel