Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari

Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari

- Gwamnan jihar Ekiti ya bayyana irin iyaka da gwamnoni ke dashi na iko duk da matsayinsu

- Ya bayyana cewa, duk da babban matsayinsa na gwamna, 'yan sanda sun sha kai mishi hari

- Ya bayyana karara cewa, kwamishinan kan iya kin maganar gwamna ya dauki ta Sufeto-janar

Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti, ya ce ya sha fama da harin ‘yan sanda, duk da matsayin sa na gwamna, Jaridar TheCable ta ruwaito.

Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Laraba yayin wani taro ta yanar gizo da Cibiyar Nazarin 'Yan Majalisa da na Dimokiradiyya ta Kasa ta shirya.

An shirya taron ne don tattauna matsalolin tsaro na Najeriya.

Ya ce kuskure ne a yarda cewa gwamnoni suna da iko mara iyaka.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun nemi a biya kudin fansan wadanda suka sace a Abuja har N200m

Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari
Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari Hoto: farmlandgrab.org
Asali: UGC

Fayemi ya ce akwai batutuwan da suka fi karfin gwamnoni duk da kasancewar sa shugaban zartarwa na jiharsa.

“Duk irin karfin da kake dashi a matsayinka na gwamna, akwai batutuwan da ba ka da iko da su saboda wannan yanki ne tsaka-tsaki kamar yadda na ambata a baya,” inji shi.

“Gwamna na iya umurtar kwamishanan 'yan sandansa amma babban sufeton ‘yan sanda (IGP) na iya gaya wa kwamishinan 'yan sandan kar ya bi wannan umarnin.

“Na yi gwamna na wani lokaci kuma na sha fama da harin 'yan sanda duk da matsayina na gwamna. Don haka bai kamata mutane su yi wani karin gishiri game da karfin gwamnoni ba.”

KU KARANTA: Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun kashe 'yan banga sama da 20 a jihar Neja

A wani labarin daban, Biyo bayan hare-haren da ake kai wa al'umomi daban-daban a wasu yankunan jihohi musamman arewacin Najeriya, lamarin ya kara karfi yayin da aka hari tawagar motocin gwamnan jihar Benue.

Wannan abin takaici ba a kan gwamnan Benue kadai ya taba faruwa ba, a tarihi an samu hare-hare kan wasu gwamnoni, ciki har da na watannin baya a jihar Borno.

Mun tattaro muku jerin gwamnonin da tsagerun maharan suka kaiwa hari, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel