‘Yan Najeriya na kashe sama da N1trn don kare kansu a duk shekara, in ji Kenny Martins

‘Yan Najeriya na kashe sama da N1trn don kare kansu a duk shekara, in ji Kenny Martins

- Cif Kenny Martins, wani jagora a Najeriya ya koka kan yadda 'yan Najeriya ke kashe kudi a tsaro

- Ya bayyana cewa, akalla ana kashe sama N1trn a duk shekara a daukar masu gadi da sauran ababen tsaro

- Ya kuma koka kan yadda aka siyasantar da harkar tsaron jama'a da dukiyoyinsu a Najeriya

Tsohon shugaban gidauniyar kayan aikin 'yan sanda, Cif Kenny Martins a ranar Alhamis ya bayyana cewa biyo bayan karuwar rashin tsaro a kasar, 'yan Najeriya daban-daban na kashe sama da N1tn a duk shekara don samar wa kansu da dukiyoyinsu tsaro.

Martins ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron lakca karo na 4 na Kamfanin Sadarwa na BAT tare da taken: "Kalubalen Tsaro da Tasirinsa kan Ci gaban Kasa," wanda aka gudanar a Otal din Sheraton da ke Legas.

Ya bukaci gwamnati da ta taka rawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kasar, Nigeria Trubute ta ruwaito.

“Kowace rana, ana mana lacca cewa tsaro nauyi ne na gama da ya rataya a kan wuyan kowa.

KU KARANTA: Wasu tsiraru ba su isa su ayyana raba mu da Najeriya ba, in Akeredolu

‘Yan Najeriya na kashe sama da N1trn don tsare kansu a duk shekara, in ji Kenny Martins
‘Yan Najeriya na kashe sama da N1trn don tsare kansu a duk shekara, in ji Kenny Martins Hoto: premiumtinesng.com

"Muna yin iyakar kokarinmu; ta amfani da dogayen gini da wayoyi masu shinge don kebe gidajenmu, tare da biyan tiriliyan duk shekara don daukar masu gadi, tare da saye da girka na’urorin tsaro masu tsada don kare kasuwancinmu, wuraren zama da muhallanmu.

“Har ila yau, muna biyan harajinnmu don kula da matakanmu uku na gwamnati, manyan ayyukansu na tsaro da Sojoji.

"Don haka, muna sa ran gwamnatocinmu a dukkan matakai za su bayar da tasu gudummawa, wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kasarmu,” inji shi.

Martins ya yi korafin cewa yawancin batutuwan tsaro a kasar na da nasaba da siyasa, yana mai cewa hakan ya sanya gazawar shugabannin siyasa wajen iya sarrafa matsalar a lokacin da lamurran suka wuce gona da iri.

KU KARANTA: Ko an raba Najeriya makiyaya ba za su kasance cikin hasara ba, Miyetti Allah

A wani labarin daban, ‘Yan bindiga sun kashe 'yan banga sama da 20 a wani hari da suka kai Kotonkoro a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Harin kamar yadda kafar yada labarai ta BBC Hausa ta ruwaito, ya faru ne a ranar Litinin bayan da 'yan banga suka yi arangama da wasu gungun 'yan bindiga a yankin.

Ibrahim Ilyasu, dan majalisar dokokin jihar daga Mariga, ya ce:

“A ranar Litinin, an yi artabu tsakanin 'yan banga da ’yan bindiga kuma suka bi su zuwa wani daji da ke kusa da su don su yake su. Abun takaici, an kashe 'yan banga kuma 'yan bindigan sun ki baiwa al'umma damar kwaso gawarwakinsu.

Source: Legit.ng

Online view pixel