EFCC ta Kama Mahaifiya da Ɗanta kan Damfara ta Intanet a Legas

EFCC ta Kama Mahaifiya da Ɗanta kan Damfara ta Intanet a Legas

- Jami'an hukumar EFCC sun kama wani mutum da mahaifiyarsa kan zargin damfarar intanet

- Wanda ake zargin ya amsa cewa ya damfari mutane kudi kimanin Naira miliyan 50 tun shekarar 2020

- An kwato kayayyaki da dama a hannunsa da suka hada da wayoyin Iphone, kwamfuta, Motoccin alfarma da sauransu

Jami'an hukumar yaki da masu almundahar kudi ta EFCC ta kama Ibeh Theophilus Uche, Shugaban 10 Kobo Wine Place da ke Ikotun a Legas tare da mahaifiyarsa kan zarginsa da damfara ta intanet na kudi kimanin Naira miliyan 50 a Legas.

An kama wanda ake zargin dan shekara 28 a Otel din Radisson Blu Anchorage da ke Victoria Island a Legas bayan samun bayannan sirri kan zarginsa da aikata laifi, rahoton Vangaurd.

EFCC ta Kama Mahaifiya da Ɗanta kan Damfara ta Intanet a Legas
EFCC ta Kama Mahaifiya da Ɗanta kan Damfara ta Intanet a Legas. Hoto: @PremiumTimesNg
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: Hisbah za ta ci ɗaliban jami'a mace da namiji da aka kama a ɗaki ɗaya tarar N20,000 kowannensu

Yayin amsa tambayoyin jami'an EFCC, Uche wanda ya ke gabatar da kansa da sunaye da suka hada da Rachael Armstrong, Keanu Reeves, Rebekah Schwarzenberger, Keanu Private, Elizabeth Hortman da Stefan Paulson ya amsa cewa yana damfarar mutane ta Bitcoin, sojan gona da sauransu.

Wanda ake zargin ya kuma amsa cewa ya damfari mutane kudin da ya kai Naira miliyan 50 tunda ya fara aikata laifuka a shekarar 2020.

Binciken da EFCC ta yi ya nuna cewa wanda ake zargin yana amfani da asusun ajiyar kudi na mahaifiyarsa a daya daga cikin bankunan zamani wurin karkatar da kudaden da ya ke samu daga laifukan.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Rundunar Soji Ta Fitar Da Sunayen Mutum 300 Waɗanda Suka Yi Nasara Da Ranar Tantancewa

Kayan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da iPhone 11 Pro Max guda daya; iPhone 12 pro max guda daya; Kwamfuta MacBook Pro guda biyu ; Game na PlayStation 5; iPad da karamar wayar Nokia.

Sauran sun hada da mota kirar Mercedes Benz S550 2015 da Lexus RX 350 SUV 2016 da wasu kayayyakin da ake zargin da kudin haramun aka siya.

Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel