Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu

Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu

- An gurfanar da wata matar aure yar kasar Kenya gaban kotu kan zargin yi wa tsohon mijinta rauni

- Matar ta ce ta tattara kayanta ta bar gidan tsohon mijin ne domin mazakutarsa ya mata girma

- Sai dai bayan ta bar gidansa ta koma nata gidan, tsohon mijin ya cigaba da kai mata ziyara amma tana korarsa

An kama wata mata yar kasar Kenya mai suna Lucy Njeri an gurfanar da ita a gaban kotu da ke Makadara kan tsohon mijinta wanda a yanzu ta ce auren ya mutu, rahoton Vanguard.

A cewar hujjar da mai karar ta gabatar a kotu, ta yi ikirarin cewa ta dade da cire tsammani kan mijinta domin duk lokacin da ya kusance ta, mazakutarsa na yi mata rauni domin ya yi girma da yawa.

Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu
Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu. Hoto: @Vangaurdngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Rundunar Soji Ta Fitar Da Sunayen Mutum 300 Waɗanda Suka Yi Nasara Da Ranar Tantancewa

Ta ce daga bisani ta gaji, ta kwashe kayanta ta bar gidasa, ta shaida masa cewa ba za ta dawo ba amma ya cigaba da zuwa gidanta yana domin duba ta duk da barazanar da ta ke masa na cewa ya dena zuwa.

An gano cewa a daren da ta watsa tsohon mijinta, Geoffrey Nyebere, acid, ya tafi gidan misalin karfe 10 na dare a ranar 16 ga watan Janairun 2021 ya fara kwankwasa kofa.

Lucy ta ce tana kan gado tare da saurayinta kuma ta ki bude masa kofa ta umurci ya fice ya bar mata harabar gida amma bai yi hakan ba ya cigaba da kwankwasa kofar, don haka sai ta bude kofa ta watsa masa acid a kirki, ta lalata masa fuska.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

Da mutane suka fara taruwa yayin da mutumin ke cikin azaba, matar da saurayinta sun tsere amma an kama su bayan kwana daya.

Shi kuma tsohon mijin an garzaya da shi asibiti don masa magani.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel