Kano: Hisbah za ta ci ɗaliban jami'a mace da namiji da aka kama a ɗaki ɗaya tarar N20,000 kowannensu

Kano: Hisbah za ta ci ɗaliban jami'a mace da namiji da aka kama a ɗaki ɗaya tarar N20,000 kowannensu

- Za a ci daliban jami'ar Bayero da ke Kano, mace da namiji tarar N20,000 kowannensu

- Hakan na zuwa ne bayan da jami'an Hukumar Hisbah suka kai sumame wani gidan dalibai suka kama su a daki daya

- Hukumar ta Hisbah ta yi wa dalibai gargadin cewa su kauracewa aikata duk wani aiki na masha'a

Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Kano: Hisbah za ta ci ɗaliban jami'a mace da namiji da aka kama a ɗaki ɗaya tarar N20,000 kowannensu
Kano: Hisbah za ta ci ɗaliban jami'a mace da namiji da aka kama a ɗaki ɗaya tarar N20,000 kowannensu. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters.

KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Lauya a Gaban Kotu Kan 'Satar Naira Miliyan 5'

"Sun fada mana cewa daga yanzu duk wani dalibi da daliba da aka kama su a daki guda za su biya tarar N20,000 kowannensu. Sun mana gargadi mu guji aikata duk wani abu na masha'a," a cewar wani dalibi.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel