Bayan dogon lokacin da ta dauka bata Aso Rock, Aisha Buhari ta gwangwaje wasu yan Najeriya

Bayan dogon lokacin da ta dauka bata Aso Rock, Aisha Buhari ta gwangwaje wasu yan Najeriya

- Matan Najeriya da matasa da dama a yanzu haka sun ci gajiyar shirin tallafi da Aisha Buhari ta kirkiro

- Uwargidan shugaban kasar a ranar Alhamis, 25 ga Maris, ta raba kayan fara aiki ga wadanda suka ci gajiyar a kokarin ta na ganin sun zama masu cin gashin kansu

- Wannan aikin alkhairin wanda ke zuwa bayan dawowar Aisha daga Dubai a kwanan nan, an fara shi ne kafin barkewar cutar COVID-19

Da alama Aisha Buhari, ta dawo daga Dubai ne tare da kyawawan abubuwan alheri ga 'yan ƙasa, musamman ga mata.

A wani taron da aka gudanar a ranar Alhamis, 25 ga watan Maris, uwargidan shugaban kasar ta baiwa mata da matasa tallafi na keken dinki, injin saka, da kuma kayan aikin noma domin kama sana’a.

KU KARANTA KUMA: 2023: Tinubu ya shiga matsala yayinda matasan Arewa suka aika sakon gargadi ga Ganduje

Bayan dogon lokacin da ta dauka bata Aso Rock, Aisha Buhari ta gwangwaje yan Najeriya
Bayan dogon lokacin da ta dauka bata Aso Rock, Aisha Buhari ta gwangwaje yan Najeriya Hoto: @aishambuhari, @Laurestar
Source: Twitter

Ofishin Aisha ne ya kirkiri wannan shirin kuma ya fara ne tun kafin billowar cutar COVID-19.

Uwargidan shugaban kasar ta yi kira da a kara samar da tsare-tsare ga mata da matasa daga gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu.

Ta ci gaba da bayyana cewa ya kamata a kammala shirin da raba kayan fara aikin.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu 'yan fashi suka sace mambobin RCCG 8

A baya mun ji cewa Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta dawo gida Najeriya bayan watanni shida a birnin Dubai, kasar haddadiyar daular Larabawa.

Legit Hausa ta samu labari daga majiya mai karfi cewa Aisha tana fadar shugaban kasa da ranan nan.

Uwargidar shugaban kasan ta tafi Dubai ne tun bayan auren diyarta, Hanan, a Satumban 2021.

A gefe guda, Yusuf Buhari, dan gidan shugaban kasa Muhammadu, na shirin angwancewa da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Ado Bayero, rahoton Daily Nigerian.

Zahra Bayero yanzu haka na karatun ilmin zanen gine-gine a kasar Birtaniya yayinda shi Yusuf Buhari ya kammala karatunsa a jami'ar Surrey, Guildford, a Birtaniya.

Majiyoyi sun bayyana cewa za'a gudanar da bikin cikin watanni biyu zuwa uku.

Source: Legit

Online view pixel