2023: Tinubu ya shiga matsala yayinda matasan Arewa suka aika sakon gargadi ga Ganduje

2023: Tinubu ya shiga matsala yayinda matasan Arewa suka aika sakon gargadi ga Ganduje

- AYCF ta gargadi Gwamna Ganduje game da yin bikin ranar haihuwar Tinubu a gidan Gwamnatin Kano

- Yerima Shettima, shugaban kungiyar na kasa, yayi wannan gargadin a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris

- Shettima yace Tinubu yayi shuru yayin da ake kaiwa ‘Yan Arewa hari a Oyo da wasu Yankin kudu maso yamma

Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta gargadi Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, kan mayar da gidan gwamnati zuwa wurin taron ranar haihuwar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Yerima Shettima, ya fitar a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris, kuma Legit.ng ta gani, AYCF ta nuna fushinta da zabin gidan Gwamnatin Kano a matsayin wurin bikin zagayowar ranar haihuwar Tinubu.

Shettima ya ce shirin cin mutunci ne ga alamar iko da gidan Gwamnatin ke da shi ga mutanen Kano tsawon shekaru da dama.

2023: Tinubu ya shiga matsala yayinda matasan Arewa suka aika sakon gargadi ga Ganduje
2023: Tinubu ya shiga matsala yayinda matasan Arewa suka aika sakon gargadi ga Ganduje Hoto: @GovUmarGanduje
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali a Kaduna yayin da wasu 'yan fashi suka sace mambobin RCCG 8

Ya ce Tinubu ya yi shiru yayin da ‘yan arewa ke fuskantar hari a Oyo da wasu sassan kudu maso yamma, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shettima ya ce:

“Yayin da aka nakasa mutane daga arewacin Najeriya yankin da Ganduje ya fito, Tinubu ya yi shiru duk da cewar ana ta lalata kadarorin‘ yan arewa a wasu sassan kudu maso yamma.

"A cikin yanayin farautar mayaƙan makiyaya, bai ma iya la'antar tashin hankalin ba. Amma duk da haka, wannan baƙon rashin kunya shine babban bako na musamman ga Ganduje a gidan Gwamnatin Kano."

A halin da ake ciki, AYCF, ta bukaci Ganduje da kar ya bari a yi amfani da shi a matsayin gwamna daya tilo a arewa wajen wofantar da alama ta daraja don bikin zagayowar ranar haihuwar dan kasa mai zaman kansa.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Masu fadi a ji ne basu ilimantar da talakawa, Amaechi

A wani labarin, mun ji cewa a daidai lokacin da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ke bayyana muradinsa na takarar shugaban kasa a 2023, ya samu karin karfin gwiwa.

Olujonwo Obasanjo wanda ‘da ne wajen tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, wanda ya yi mulki sau biyu a 1976 da 1999, ya goyi bayan APC a zaben 2019.

Jaridar Vanguard ta ce Mista Olujonwo Obasanjo ya shiga sahun masu goyon bayan Yahaya Bello ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2003.

Asali: Legit.ng

Online view pixel