Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Tijjaniya na duniya, Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Tijjaniya na duniya, Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass

- Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Tijjaniya na duniya , Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass

- Khalifa Mahy Nyass ya kai ziyara fadar Shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja a yau Juma’a, 26 ga watan Maris

- Hadimin Shugaban kasa Bashir Ahmed ya tabbatar da ganawar shugabannin biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi baƙuncin Shugaban Tijjaniya na duniy,a Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass.

Khalifa Mahy Nyass da tawagarsa sun isa fadar Shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, 26 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: An yankewa wani mutum hukuncin shekara guda a gidan yari kan sata a coci

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Tijjaniya na duniya, Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban Tijjaniya na duniya, Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Mai taimakawa Shugaban kasa Buhari a shafukan zumuntar zamani, Bashir Ahmad ne ya sanar da labarin ganawar tasu tare da wallafa hotunan ganawar a shafinsa na Twitter.

Ya ce:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Nyass, Khalifan Sheikh Ibrahim Nyass (RTA) a fadar Shugaban kasa, Abuja.”

KU KARANTA KUMA: An gina daular kasuwancin Aliko Dangote ne daga rancen da ya karba daga kawunsa

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus) a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a bangaren kafar watsa labarai, Bashir Ahmad ya sanar da hakan cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter @BashirAhmaad.

Har wa yau, a wani taron na daban, a ranar Juma'a, Shugaba Buhari ya gana da shugaban hukumar Yaki da Fatauci da Shan Miyagun Kwayoyi, NDLEA, Mohammed Buba Marwa a Aso Rock.

Duk da cewa hadimin shugaban kasar bai bayyana abinda za a tattauna yayin ganawar ba, Legit.ng na ganin akwai yiwuwar ziyarar na da alaka da kallabalen tsaro da ke adabar kasar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng