An yankewa wani mutum hukuncin shekara guda a gidan yari kan sata a coci

An yankewa wani mutum hukuncin shekara guda a gidan yari kan sata a coci

- Kotun Majistare da ke Abeokuta, a ranar Juma’a, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 21, Afolabi Samuel, hukuncin daurin shekara daya

- An kama matashin da laifin satar waya da kuma damin kudi har N52,000

- Samuel ya afka cikin cocin ta taga a yayinda ake addu'an dare sannan ya kwashe abubuwan da ake tuhumarsa a kai

Wata kotun Majistare da ke Abeokuta, a ranar Juma’a, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 21, Afolabi Samuel, hukuncin shekara daya a gidan yari saboda satar wayar Tecno da kudin ta kai N76,000 da tsabar kudi N52,000.

Samuel, wanda babu cikakken adireshin sa, ya amsa tuhume-tuhume guda biyu da ake masa na sata.

Alkalin Kotun, Mista D.S Ogongo, ya ce duk wasu shaidu da aka gabatar a kotu sun tabbatar da cewa wanda ake karan ya aikata laifin.

An yankewa wani mutum hukuncin shekara guda a gidan yari kan sata a coci
An yankewa wani mutum hukuncin shekara guda a gidan yari kan sata a coci Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: An gina daular kasuwancin Aliko Dangote ne daga rancen da ya karba daga kawunsa

Saboda haka, Ogongo, ya yanke wa Samuel hukuncin ɗaurin shekara guda ba tare da zaɓi na tara ba.

Tun da farko, mai gabatar da kara, sufeto Olaide Rawlings, ya fadawa kotu cewa mai laifin ya aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Fabrairu a Cocin Celestial of Christ, Itunu Parish da ke yankin Ilawo cikin Abeokuta.

Rawlings ya ce wanda ake tuhuma, a tsakar dare lokacin ana addu’a, ya fasa tare da shiga cocin ta taga sannan ya saci wayar Techno Camon-16 da kudin ta ya kai N76,000, mallakar Mista Ganiu Adeola.

Ta fadawa kotun cewa mai laifin ya kuma saci kudi N52,000, mallakin wani Mista Dairo Theophilus.

Duk abubuwan, in ji ta, an kiyasta su a kan N128,000, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ta kara da cewa an kama mai laifin ne da taimakon wata na’urar bin diddigin waya, wanda hakan ya sa aka cafke shi.

KU KARANTA KUMA: Yana da matukar wuya a siyar da gurbataccen kaya, Baba-Ahmed ya yi wa Garba Shehu ba’a a shirin talbijin

Mai gabatar da karar ya ce laifukan sun sabawa sashi na 415, 383 da 390 (9) na kundin manyan laifuka Vol. 1, Dokokin Ogun, 2006.

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun cafke wasu mutane uku 'yan damfara waɗan da ke damfarar mutane da sunan cewa su aljanu ne.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya bayyana sunayen mutanen; Usman Adamu, 40, Abba Ibrahim, 38, da kuma Abdurrauf Iliyasu, 39.

SP Gambo yace an sami nasarar kama waɗan da ake zargin ne bayan sun kira wata mata mai suna Jamila Sulaiman a waya sun umarce ta da taje kan hanyar fita garin Yar Gamji ta aje kuɗi N150,000.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng