Yan Sanda Sun cafke Wasu 'Yan Damfara Uku Da 'Yan Bindiga Biyu a Katsina

Yan Sanda Sun cafke Wasu 'Yan Damfara Uku Da 'Yan Bindiga Biyu a Katsina

- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta samu nasarar cafke wasu yan damfara su uku.

- Yan damfaran na kiran mutane a waya su basu tsoro da cewa su aljanu ne su biya kuɗi ko su kashe wani nasu

- Mai magana da yawun yan sandan jihar ya bayyana cewa sun kama su ne bayan sunyi makamancin haka ga wata mata

Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun cafke wasu mutane uku 'yan damfara waɗan da ke damfarar mutane da sunan cewa su aljanu ne.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya bayyana sunayen mutanen; Usman Adamu, 40, Abba Ibrahim, 38, da kuma Abdurrauf Iliyasu, 39.

KARANTA ANAN: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sabunta Naɗin Shugaban Hukumar BPE

SP Gambo yace an sami nasarar kama waɗan da ake zargin ne bayan sun kira wata mata mai suna Jamila Sulaiman a waya sun umarce ta da taje kan hanyar fita garin Yar Gamji ta aje kuɗi N150,000.

Sun tsorata matar da cewa su "aljanu" ne idan kuma batayi abinda suka saka ta ba to zasu saka rayuwar mahaifanta ko kuma 'yayanta a cikin hatsari ko su kashe su.

Matar ta tsorata matuƙa, hakan tasa ta ɗauki maƙudan kuɗaɗen da suka buƙata taje ta aje musu a inda suka ce.

Sannan kuma ta tura musu N97,000 a bankin ɗaya daga cikinsu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Yan Sanda Sun cafke Wasu 'Yan Damfara Uku Da 'Yan Bindiga Biyu a Katsina
Yan Sanda Sun cafke Wasu 'Yan Damfara Uku Da 'Yan Bindiga Biyu a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A lokacin da yan sanda suka fara bincike "Mun bibiyesu kuma muka kama su" kuma sun amsa laifin su dama waɗansu laifukan daban "Muna cigaba da bincike" inji shi.

KARANTA ANAN: Kano: Dole 'yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara

Rundunar yan sandan ta kuma ce ta samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin 'yan bindiga ne; Hassan Magu, 20, da Salisu Lado, 25.

An kama mutanen biyu ya yin da suke kan hanyar su ta zuwa yankin karamar hukumar Ɗan-dume domin kai hari.

SP Gambo Isa ya ce mutanen biyu sun amsa laifin su kuma sun ce suna daga cikin waɗan da ke aiki a yankunan jihohin Katsina, Zamfara da kuma Kaduna.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kashe mutum 12 a sabbin hare-hare da suka kai garuruwan Kaduna da Sokoto

Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare- hare da aka kai wasu jihohin arewa guda biyu.

Abubuwan na bakin ciki sun faru ne a Kaduna da Sokoto a ranar Laraba, 24 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262