Na gano ‘Yan bindigan da su ka sace Dalibai 38 a Kaduna, a ban damar zama da su inji Gumi

Na gano ‘Yan bindigan da su ka sace Dalibai 38 a Kaduna, a ban damar zama da su inji Gumi

- Sheikh Ahmad Gumi ya ce ya gano wadanda su ka sace Dalibai 38 a Afaka

- Gumi ya kuma bayyana abin da ya hana a saki wadannan ‘yan makarantan

- Shehin ya ce umarnin da aka ba jami’an ya hana a iya zama da ‘yan bindiga

Shahararren malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana game da wasu daliban makarantun gandu ta Kaduna da aka yi garkuwa da su.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce umarnin da aka ba jami’an tsaro na harbe duk wanda su ka gani ya na dauke da bindigar AK-47 ya sa aka gaza ceto daliban.

Da yake magana da Daily Trust, malamin ya ce ya hadu da wasu ‘yan bindiga da su ka taimaka masa har ya gano gungun wadanda su ka sace wadannan dalibai.

KU KARANTA: Iyayen ɗalibai 39 da aka sace a Afaka sun yi zanga-zanga

Babban shehin yake cewa duk da ya gano shugaban ‘yan bindigan da ke da hannu wajen wannan danyen aiki, amma yunkurin zama da shi bai haifar da ‘da mai ido ba.

Malamin fikihun ya ce abin da ya hana shi zama da wadannan miyagu da nufin a kubutar da daliban shi ne umarnin harbe masu rike AK-47 da shugaban kasa ya bada.

Haka zalika malamin ya bayyana cewa ba don wasu jami’an gwamnati ba su bada goyon-baya ba, da ya yi sanadiyyar da mafi yawan ‘yan bindiga za su ajiye makamansu.

Shehin ya ce: “Yanzu haka mun kai ga gano wadanda su ka yi wannan ta’adi. Mun gano shugabansu da ya dauke daliban, amma bai taba zaman sulhu da mu ba.”

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun saki bidiyon daliban da aka sace a Kaduna

Na gano ‘Yan bindigan da su ka sace Dalibai 38 a Kaduna, a ban damar zama da su inji Gumi
Ahmad Gumi Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

“Gungun da mu ka samu, sun bayyana mana shi, amma ba mu iya tuntubarsa ba saboda lamarin tsaro tun da gwamnati ta bada umarnin a harbe duk wanda aka samu.”

Dr. Gumi ya cigaba: “Sannan bayan nan, gwamnati ta ce babu maganar sulhu. Saboda haka ba na so in shiga daji, gwamnati ta ce mu na kashe mata kwarin-gwiwa.”

Sheikh Gumi ya ba gwamnati shawara ta kyale su, su shiga su yi sulhu domin a ceto yaran nan. Malamin ya ce ya na wannan aiki ne don kansa ba wata jam’iyya ba.

Dazu kun ji kungiyar manyan Arewa ta sake ragargazar Gwamnatin APC mai-ci, ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gaza idan ana maganar rashin tsaro.

Da yake magana a jiya, darektan yada labarai da wayar da kai na kungiyar Northern Elders’ Forum, Hakeem Baba-Ahmed, shugaba Buhari ya gagara shawo kan kasar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng