Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka

Afirka nahiya ce da Allah ya albarkace ta da manyan hazikai da kuma hamshakan 'yan kasuwa da ke mamaye duniya, kuma saboda nasarorin da suka samu, wadannan attajiran suna karfafa gwiwar mutane masu tasowa don cimma nasara.

A kan haka, Legit.ng ta kawo maku mutane bakwai mafi kudi a Afirka a 2021, kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa.

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

1. Aliko Dangote

Aliko Dangote shine mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika wanda ya mallaki dala biliyan $ 12.1 (N4,608,527,000,000). Mutumin mai shekaru 63 ya samar da kamfanin kera siminti mafi girma a Afirka wanda ake kira Dangote Cement.

Attajirin kuma mai aikin taimako yana da matatar mai da aka fara aikinta tun shekarar 2016 kuma ana sa ran zata kasance daya daga cikin manyan matatun mai a duniya da zarar an kammala ta.

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka Hoto: Wei Leng Tay/Bloomberg
Asali: Getty Images

2. Nassef Sawiris

Nassef Sawiris ya fito daga kasar Masar kuma yana gudanar da kamfanin OCI, daya daga cikin manyan masu samar da takin nitrogen a duniya, tare da shuke-shuke a Texas da Iowa.

Attajirin dan kasuwar na Masar yana da zunzurutun kudi dala biliyan 8.5 (N3,237,395,000,000).

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka Hoto: Mikhail Metzel/TASS
Asali: Getty Images

3. Nicky Oppenheimer and family

Nicky Oppenheimer wani dan kasuwa ne dan Afirka ta Kudu wanda ya sayar da hannun jarinsa kaso 40% a kamfanin na lu’u-lu’u na De Beers ga kungiyar Anglo American da ke hakar ma'adinai kan dala biliyan 5.1 (N1,942,437,000,000) a tsabar kudi a shekarar 2012.

Attajirin mai shekaru 75 shine tsara na uku na dangin sa da suka gudanar da DeBeers, kuma ya ɗauki kamfanin a mai zaman kansa a cikin 2001.

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka Hoto: Jeff Overs/BBC News & Current Affairs
Asali: Getty Images

4. Johann Rupert and family

Attajirin dan Afirka ta Kudu shi ne shugaban kamfanin Compagnie Financiere Richemont.

Dan kasuwar mai shekaru 70 ya mallaki kaso 7% na kamfanin hadahadar kudade na Remgro, wanda yake jagoranta, da kuma kashi 25% na kamfanin Reinet, wanda yake da hannun jari.

Ya mallaki $ 7.2 biliyan (N2,742,264,000,000).

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka Hoto: David Cannon
Asali: Getty Images

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana

5. Mike Adenuga

Mike Adenuga shine na biyar a jerin masu kudi a Afirka kuma na biyu a Najeriya. Adenuga, wanda ya mallaki dala biliyan 6.6 (N2,513,742,000,000), ya gina arzikin sa a fannin sadarwa da samar da mai.

Mutumin mai shekaru 67 ya mallaki kamfanin Globacom, wanda shi ne na uku a yawan kamfanonin sadarwa a Najeriya.

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka Hoto: Andrew Esiebo/Icon Sport
Asali: Getty Images

6. Abdulsamad Rabiu

Abdulsamad Rabiu ya fito daga Najeriya kuma shine ya kirkiri kungiyar BUA. Yana kasuwancinsa ne a harkar samar da siminti, sarrafa sikari da kuma gine-gine.

Mutumin mai shekaru 60 yana da kimanin dala biliyan $ 5.5 (N2,094,785,000,000).

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka Hoto: @buagroup_ng
Asali: Instagram

7. Issad Rebrab and family

Issad Rebrab dan Algeria ne kuma shi ne ya kafa kuma shine babban jami’in gudanarwa na Cevital, babbar kamfanin Aljeriya mai zaman kansa.

Kamfanin yana da daya daga cikin manyan matatun mai a duniya, tare da ƙarfin samar da tan miliyan 2 a shekara.

Issad yana da shekaru 77 kuma arzikinsa ya kai kimanin dala biliyan $ 4.8 (N1,828,176,000,000).

Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka
Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka Hoto: Issouf Sanogo/AFP
Asali: Getty Images

A wani labari, kungiyar zamantakewar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hure, ta ce makiyaya ba za su kasance cikin wahala ba idan aka raba Najeriya.

Mai magana da yawun kungiyar, Saleh Alhassan, ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake gabatarwa a wani shirin jaridar Punch wato The Roundtable.

A cewarsa, gwamnonin arewa za su bunkasa harkar kiwon dabbobi idan suka daina samun "kudin mai" daga Gwamnatin Tarayya.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel